Month: June 2021

‘Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin Ganduje, ‘yan sanda uku sun jikkata

‘Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin Ganduje, ‘yan sanda uku sun jikkata

Daga IBRAHIM HAMISU 'Yan bindiga sun kai wa tawagar motocin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, hari ran Talata da daddare a kan hanyarsu ta komawa Kano daga Zamfara. Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa harin ya yi sanadiyar jikkata wasu 'yan sanda uku daga tawagar. Bayanai sun nuna yayin harin, Gwamna Ganduje na cikin motar gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru tare da shi. Majiyar Manjaha ta bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da ke cikin tawagar da kuma 'yan bindigar inda wasu 'yan sanda uku suka ji rauni sakamakon harbin bindiga.
Read More
Sauya sheƙa: Ƙofarmu a buɗe take ga masu son dawowa APC – Buhari

Sauya sheƙa: Ƙofarmu a buɗe take ga masu son dawowa APC – Buhari

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ƙofar jam'iyyarsu ta APC a buɗe take ga duk ɗan siyasar da ke sha'awar sauya sheƙa zuwa APC mai mulki. Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook ran Laraba a matsayin tsokaci dangane da sauya sheƙa da Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi kwanan nan daga PDP zuwa APC. Buhari ya ce dawowar Matawalle APC ya nuna cewa ƙudurin shugabanci nagari da suke da shi shi ne dalilin da ya sa 'yan Nijeriya ke ta rungumar APC. Don haka ne shugaban ya ce, "Bari in faɗa ƙarara cewa…
Read More
Fursunoni huɗu sun samu shaidar digiri bayan kammala karatu a NOUN

Fursunoni huɗu sun samu shaidar digiri bayan kammala karatu a NOUN

Daga BASHIR ISAH Wasu fursunoni huɗu daga gidan gyaran hali da ke yankin Kuje a birnin tarayya Abuja, kowannensu ya samu shaidar digiri bayan kammala karatu a Buɗaɗɗiyar Jami'ar Nijeriya (NOUN). Kwanturola mai kula da gidan gyaran hali na Abuja, Abdul-rahman Maiyaki ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye ɗaliban wanda ya gudana a Talatar da ta gabata a Abuja. Tare da cewa cibiyoyin gyaran hali wurare ne da ake gayara ɗabi'un fursunoni don kyautata musu rayuwa. Maiyaki ya ƙara da cewa cibiyar wuri ne da ake gyara halayen fursunoni domin su koma su zama nagartattu a cikin al'umma. Daga…
Read More
Minista ta raba takardun kama aiki da komfutoci 172 ga masu sa ido kan ayyukan inganta rayuwa a Sokoto

Minista ta raba takardun kama aiki da komfutoci 172 ga masu sa ido kan ayyukan inganta rayuwa a Sokoto

Daga UMAR M. GOMBE Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta miƙa takardun kama aiki da ƙananan komfutoci ga ma'aikata 172 waɗanda aka ɗauka domin su sanya ido kan ayyukan inganta rayuwa da ma'aikatar ta ke aiwatarwa a Jihar Sokoto. A wajen taron raba takardun da komfutocin, ministar ta ce, “Wannan ma'aikata ta ƙaddamar da horas da ma'aikata 5,000 masu zaman kan su da za su sa ido kan ayyukan shirin Haɓaka Rayuwar Al'umma (National Social Investment Programme, NSIP) a Abuja a ranar Alhamis, 4 ga Fabrairu, 2021. An gudanar da horaswar a duk faɗin…
Read More
Me za mu yi kan tsadar abinci?

Me za mu yi kan tsadar abinci?

Daga MARHABA YUSUF ALI Wai jama'a bai kamata mu dage da maganar tsadar kayan abinci ba kamar yadda muka dage da maganar tsaro kuwa? Idan kai ka ci ka ƙoshi ba ka tuna wanda tun kafin rayuwar ta yi tsada da ƙyar suke samun abinda za su ci ma balle yanzu da komai ya tashi wani ma ya ninka? Magidanta da suka ajiye iyali a gida su wuni suna yawo a rana wani da ƙyar zai samu abin da zai ciyar da su sau ɗaya a rana. Wani jarin ma bai kai na dubu biyu ba, me ya samu? Me…
Read More
Raina kotu ya janyo wa Jacob Zuma zaman gidan yari na watanni 15

Raina kotu ya janyo wa Jacob Zuma zaman gidan yari na watanni 15

Babbar kotun ƙasar Afirka ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma hukuncin zaman gidan yari na watanni 15, bayan samunsa da aikata laifin raina kotu, biyo bayan ƙin bayyana a gaban masu binciken zargin rashawa da aka yi masa. An shaida wa Zuma cewa ya miƙa kansa nan da kwanaki 5, kuma idan ya ƙi yin biyayya za a umurci ‘yan sanda su tisa ƙeyarsa zuwa kurkuku. Wannan hukunci abu ne da ba a saba gani ba kuma cike yake da tarihi, don kuwa ya zama abin misali ga Afirka ta Kudu da ma nahiyar Afirka baki…
Read More
Yadda bikin komawar Matawalle APC ya kasance

Yadda bikin komawar Matawalle APC ya kasance

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A wannan Talatar Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya sauya sheƙa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma All Progressive Congress (APC) jam'iyya mai mulki a ƙasar nan. Da yake jawabi a yayin bikin sauya shelarsa zuwa APC, da aka gudanar a katafariyar kasuwar baje koli ta Zamfara da ke Gusau, Matawalle ya ce yanzu shi ne shugaban APC a Zamfara. Matawalle ya yi kira ga dukkan mambobi da magoya bayan APC a jihar da su haɗa kai su gina sabuwar Zamfara da APC gabanin babban zaɓen 2023. Matawalle ya yaba wa Shugaban…
Read More
Gwamnati ta rusa gidajen masu garkuwa da mutane a Binuwai

Gwamnati ta rusa gidajen masu garkuwa da mutane a Binuwai

Daga WAKILINMU Bayanai daga Jihar Binuwai sun nuna gwamnatin jihar ta rusa wasu gidaje guda biyu waɗanda ake zargin mallakar wani mai harkar satar mutane ne mai suna Aondofa Cephas Chekele wanda aka fi sani da Azonto. A ranar Litinin da ta gabata gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rusa gidajen domin ya zama gargaɗi ga waɗanda ke hana zaman lafiya zama da gidinta a jihar. Binciken Manhaja ya gano cewa Azonto shi ne mataimakin gawurtacen ɗan bindigar nan da aka kashe a jihar a Satumban 2020, wato Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana. 'Yan sanda ne suka jagoranci…
Read More
NNPC ya bayyana dalilinsa na neman sayen kaso a matatar man Ɗangote

NNPC ya bayyana dalilinsa na neman sayen kaso a matatar man Ɗangote

Daga UMAR M. GOMBE Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayyana dalilin da ya sa yake neman sayen wani kaso a matatar mai na Ɗangote. NNPC ya bayyana hakan ne ta bakin shugabansa Mele Kyari, yayin wani shirin talabijin da aka yi da shi a tashar ChannelsTV a ranar Talata. Ya zuwa 2022 ake sa ran matatar Ɗangote ta soma aiki inda za ta riƙa tace mai har ganga 650,000 a kowace rana. Lamarin da ake kallo da muhimmiyar cigaba a fannin makamashi a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya. Tun a Mayun da ya gabata NNPC ya bayyana…
Read More
Nnamdi Kanu ya sake faɗawa komar Gwamnatin Nijeriya

Nnamdi Kanu ya sake faɗawa komar Gwamnatin Nijeriya

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Nijeriya ta sake cafke jagoran masu rajin kafa Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu. Bayanai sun nuna an samu nasarar cafke Kanu ne albarkacin wani aikin haɗin gwiwa da aka yi tsakanin Nijeriya da hukumomin tsaron ƙetare. Kafin wannan lokaci dai, Nijeriya ta shafe shekaru biyu tana neman Nnamdi Kanu ruwa a jallo inda ya tsare neman mafaka a ƙetare. Babbabn lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya tabbatar da kama Nnamdi Kanu a ranar Talata yayin wani taron manema labarai na gaggawa da ya gudana a ofishinsa da ke Abuja. Kanu wanda ke fuskantar shari'a kan…
Read More