Month: June 2021

Majalisar Wakilai ta karɓi buƙatar Buhari kan neman ƙarin kasafi na bilyan N896

Majalisar Wakilai ta karɓi buƙatar Buhari kan neman ƙarin kasafi na bilyan N896

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talata Majalisar Wakilai ta Tarayya ta karɓi bukatar Shugaban Ƙasa Muhammadu kan buƙatar neman ƙarin kasafin 2021 da ya gabatar. Buhari ya buƙaci ƙarin kasafi na Naira bilyan 895.8 ne domin yauƙaƙa kasafin 2021. An ce ƙarin kasafin da Buhari ya nema za a a yi amfani da shi ne wajen ƙara wa sojoji kayan aiki da bunƙasa shirin rigakafin korona da na yaƙi da cutar HIV. A makon da ya gabata Majalisar Datawa ta yi nazarin buƙatar ƙarin kasafin da Shugaba Buhari ya gabatar mata a mataki na biyu.
Read More
Shinkafi, ciyamomin APGA 14 da na mazaɓu 147 sun bar APGA zuwa APC a Zamfara

Shinkafi, ciyamomin APGA 14 da na mazaɓu 147 sun bar APGA zuwa APC a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban Sakataren Kwamitin amintattun na ƙasa na Jam'iyyar APGA, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi tare da shugabannin ƙananan hukumomi 14, na Jami'iyyar, shugabannin mazaɓu 147 a jihar Zamfara sun fice daga jam’iyyarsu ta APGA kuma sun bi gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle zuwa Jami'iyyar APC mai mulki a ƙasar nan. Shinkafi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a gidansa da ke Gusau yayin da yake jawabi ga shugabannin zartarwar jihar na APGA wanda ya haɗa da dukkanin shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi 14, shuwagabannin mazaɓu 147 waɗanda su duka suka sauya sheƙa daga jam’iyyarsu…
Read More
Sun harbe mai juna-biyu sun yi garkuwa da mijinta a Kwara

Sun harbe mai juna-biyu sun yi garkuwa da mijinta a Kwara

Daga AISHA ASAS Rahotanni daga jihar Kwara sun tabbatar cewa a ranar Asabar da ta gabata, wasu 'yan bindiga sun harbe wata mai juna-biyu har lahira kana suka yi garkuwa da magidanta. Lamarin wanda ya auku a yankin ƙaramar hukumar Offa na jihar, an ce 'yan bindigar sun harbe Hawa ɗauke da juna-biyu sanan suka yi awon gaba da maigidanta, Lukman Ibrahim. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna mummunan al'amarin ya auku ne a daidai lokacin da Lukman da surikinsa da matar tasa da kuma wani ɗansa suke mota za su koma gida ran Asabar da daddare. Sahaidu sun…
Read More
IPMAN ta musanta shirin tafiya yajin aiki

IPMAN ta musanta shirin tafiya yajin aiki

*Alhaji Fari ya buƙaci 'yan ƙasa su kwantar da hankalinsu Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar 'Yan Kasuwar Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (IPMAN) ta ce ba ta da wani shirin shiga yajin aiki ko aniyar rufe gidajen mai a faɗin ƙasa. Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Alhaji Sanusi Fari, shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Awka wadda ta sami sa hannun sakatarenta na ƙasa, Mr Chidi Nnubia, Fari ya buƙaci al'ummar ƙasa da su yi watsi da duk wani bayani da ke nuni da IPMAN na shirin tafiya yajin aiki.…
Read More
Gobe Talata Matawalle zai yi bikin komawa APC

Gobe Talata Matawalle zai yi bikin komawa APC

Daga WAKILINMU Gobe Talata idan Allah ya kai mu Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Babban daraktan gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Gusau a Lahadin da ta gabata. A cewar Idiris, "An kammala shiri na sauya sheƙar gwamnanmu daga PDP zuwa APC. "Baki ɗayan kwamitocin da aka kakkafa domin bikin duk sun ba da bayanin komai na tafiya daidai don tabbatar da bikin ya gudana ciki nasara a Gusau a ranar Talata, 29, Yuni." Ya ƙara da cewa komawar…
Read More
NDLEA ta cafke masu fataucin miyagun ƙwayoyi 363 a Jigawa

NDLEA ta cafke masu fataucin miyagun ƙwayoyi 363 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Hukumar Hana Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen jahar jigawa, ta sami nasarar kama masu shaye-shaye mutun 363 a faɗin jahar. Kwamandar hukumar a jihar Jigawa, Hania Maryam Gambo Sani, ita ce ta tabbatar faruwar hakan, inda ta ce sun cafke masu laifin ne tsakanin Yulin shekarar da ta gabata zuwa 15 ga Yunin 2021. Maryam ta bayyana haka ne awani taron manema labarai da ta kira a ranar Asabar da ta gabata a matsayin wani ɓangare na abikin ranar hana shan miyagun ƙwayoyi ta duniya da aka gabatar a Dutse,…
Read More
Matawalle: PDP ta rasa APC ta samu

Matawalle: PDP ta rasa APC ta samu

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan sha'anin kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ne ya yi nuni da hakan a shafinsa na Facebook a Lahadin da ta gabata. Inda ya wallafa cewa, "Ashe Zamfara ta dawo gida! Barka da zuwa Matawalle." Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, Matawalle bai fito ya tabbatar da sauyin sheƙar nasa a hukumance ba.
Read More
Zulum ya dakatar da wata cibiyar Faransa saboda shirin koyar da harbi da bindiga a otel a Maiduguri

Zulum ya dakatar da wata cibiyar Faransa saboda shirin koyar da harbi da bindiga a otel a Maiduguri

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya bada umarnin dakatar da cibiyar ACTED ta ƙasa da ƙasa mai zaman kanta bayan da aka gano cibiyar na gudanar da harkar horar da wasu mutane yadda ake harbin bindiga a cikin wani otel da ke Maiduguri. Mai magana da yawun gwaman, Malam Isa Gusau, shi ne ya bayyana umarnin da Zulum ya bayar, tare da cewa cibiyar wadda ta ƙasar Faransa ce, an same ta tana amfani da bindigogin roba wajen bada horo kan yadda ake harbi da bindiga a wani otel a Maiduguri. Gusau ya ce, mazauna yankin sun…
Read More
Rajistar masu zaɓe: INEC ta ƙaddamar da gidan yana yayin damuwa kan tsaro

Rajistar masu zaɓe: INEC ta ƙaddamar da gidan yana yayin damuwa kan tsaro

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za a fara aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR) a ranar 19 ga Yuli. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taro da ya yi da manema labarai tare da ƙaddamar da gidan yana na musamman don aikin rajistar masu zaɓen a ranar Alhamis a Abuja. Yakubu ya ce a yayin da za a soma aikin rajistar ta hanyar yanar gizo a ranar 28 ga Yuni a duk faɗin ƙasar nan, za a fara aikin a…
Read More
Ƙungiyar Matasan Arewa ta nemi tubarrakin Kansilan Kano

Ƙungiyar Matasan Arewa ta nemi tubarrakin Kansilan Kano

Daga SANI AHMAD GIWA A jiya Juma'a 25 ga Yuni, 2021, ne wata ƙungiyar matasan Arewa mai suna Arewa Youths Elites Initiative ta yi tattaki tun daga Kaduna ta kai wa fitaccen kansilan nan na Kano mai mataimaka 18, Hon. Muslihu Yusuf Ali, ziyarar ban girma da neman tubarraki, inda ta miƙa ma sa takardar naɗa shi Uban Ƙungiya (wato Grand Patron), saboda shi himmarsa da ƙoƙarinsa wajen inganta rayuwar al'umma, musamman ma matasa. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa, wacce Kakakin yaƙin neman zaɓen kansilan, Muhseen Tasiu Yau, ya fitar a jiyan, ya na mai tabbatar da…
Read More