Month: June 2021

Me ya sa DSS ta gayyaci Sheikh Gumi?

Me ya sa DSS ta gayyaci Sheikh Gumi?

Bayanan da Manhaja ta samu sun nuna hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci fitaccen malamin nan, wato Sheikh Ahmed Gumi. Duk da dai ba a bayyana dalilin gayyatar da DSS ta yi wa malamin ba, amma dai ya tabbata cewa ta gayyace shi. Sai daiwasu 'yan ƙasa na ra'ayin cewa gayyatar ba ta rasa nasaba da yadda malamin ke ƙoƙarin ziyartar 'yan fashin dajin da suka addabi sassan ƙasa tare da bai wa gwamnatin shawarwari don samun masla. Mai magana da yawun DSS,, Dr. Peter Afunanya, ya tabbatar wa jaridar The Fender cewa gaskiya ne cewa hukumarsu ta gayyaci Sheikh…
Read More
Yawaitar laifuka a Nijeriya ya wuce minsharrin – Ganduje

Yawaitar laifuka a Nijeriya ya wuce minsharrin – Ganduje

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa, afkuwar laifuka a jihar Kano, shi ma ya haura ya zuwa mataki na gaba. Wato dai ya wuce hankali. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin Sufeto Janar na hukumar 'yansanda, Usman Baba a jihar Kano. Gwamnan ya ƙara da cewa, idan za a kula, za a ga ya baza na'urorin leƙen asiri CCTV a ko'ina a jihar Kano. Saboda kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar. Ganduje ya bayyana cewa tunda su ma afkuwar laifuka sun yawaita, dole ne a samo karen bana…
Read More
Arahar fetur ta yi yawa a Nijeriya – NNPC

Arahar fetur ta yi yawa a Nijeriya – NNPC

*Ya kamata farashin fetur ya kai Naira 256 duk lita*Nijeriya na kashe Naira biliyan 150 duk wata kan tallafin mai – Mele Kyari*Nijeriya ba za ta iya jure biyan tallafin mai ba, inji shi Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Babban Manajan Darakta na kamfanin kula da mai na Nijeriya (NNPC), Malam Mele Kyari, ya bayyana cewa, bisa la’akari da irin kuɗin da Nijeriya ke kashewa wajen shigo da tataccen man fetur a ƙasar, za a iya cewa, farashinsa na Naira 162 a gwamnatance ya yi matuƙar kaɗan, yana mai cewa, aƙalla ya kamata a sayar da shi kan Naira…
Read More
Da ɗuminsa: Buhari ya soke tafiya duba lafiyarsa a Landon

Da ɗuminsa: Buhari ya soke tafiya duba lafiyarsa a Landon

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da tafiyar da ya kamata ya yi yau Juma'a zuwa Birnin Landon domin duba lafiyarsa. A bayanin da mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasar kan yaɗa labarai, Femi Adesina, ya fitar ya ce za a sanar da wata ranar da ta dace domin tafiyar. Sai dai a bayaninsa bai sanar da dalilin dakatar da tafiyar ba, lamarin da 'yan Nijeriya da dama ke son sani, kasancewar ruwa ba ya tsami banza.
Read More
Ganduje zai gina gidaje 5,000 ga malaman makaranta

Ganduje zai gina gidaje 5,000 ga malaman makaranta

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Kano da wani kamfani mai zaman kansa, da nufin gina gidaje 5,000 ga malaman makaranta a jihar. Rahotanni sun tabbatar da cewa an cimma wanan matsaya ne yayin wani taro da aka gudanar a masaukin gwamnonin ƙasar nan da ke rukunin gidaje na Asokoro a Birnin tarayya Abuja. Yayin wannan taron da kamfanin, Gwamna Ganduje ya na tare ne da Sanatocin Kano guda 3, kwamishinoni, 'yan majalisu da sauran muƙarraban gwamnati. Sakataren yaɗa labaran Gwamnan, Malam Abba Anwar,…
Read More
Gaskiyar magana game da rashin samun miji ko matar aure

Gaskiyar magana game da rashin samun miji ko matar aure

Daga AMINA YUSUF ALI Wannan maudu'i da za mu tattauna wannan mako, za mu duba yadda ake yawaitar samun samari da 'yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Ƙasashen Hausa cike suke da waɗannan matsaloli. Kuma kowa ka taɓa cikin waɗannan matasan sai ya ce ai ya rasa miji ko matar aure ne. Wasu lokutan ma har a kafafen sadarwa ko dandalin sada zumunta na yanar gizo daban-daban za ka ga an ba da cigiyar mutum yana neman matar aure iri kaza, ko mai kama kaza. Haka su ma matan sukan ɓoye sunansu na ainahi su tallata kansu a waɗancan kafafen…
Read More
Faruk Lawan: Ina aka kwana kan babban batun?

Faruk Lawan: Ina aka kwana kan babban batun?

A tsakiyar makon nan ne wata Babbar Kotu a Abuja ta yanke wa fitaccen tsohon ɗan Majalisar Wakilai na Tarayyar Nijeriya, Hon. Faruk Lawan, hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bayan da ta ce kama shi da laifin amsar na goro daga hannun wani babban attajiri kuma ƙasurgumin ɗan kasuwa a ƙasar, wato Mista Femi Otedola a shekara ta 2012 lokacin da Lawan ]in ke shugabantar Kwamitin Bincike kan Badaƙalar Tallafin Man Fetur. A yayin da ta ke yanke hukuncin, alaƙalin kotun, Mai Shari’a Angela Otaluka, ta ce, Hon. Lawan ya kasa tabbatar wa da kotu iƙirarinsa na cewa,…
Read More
Kyawun alƙawari: Buhari ya yi wa Tawagar Super Eagles a gasar Tunisiya 1994 kyautar gidaje

Kyawun alƙawari: Buhari ya yi wa Tawagar Super Eagles a gasar Tunisiya 1994 kyautar gidaje

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a ba da kyautar gida mai ciki uku-uku ga kowane ɗan wasan Super Eagle na tawagar da ta ciyo wa Nijeriya Kofin Afirka a gasar da aka gudanar a ƙasar Tunisiya a 1994. Wannan kyauta na mazaunin cika alƙawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa 'yan wasan ne a wancan lokaci sakamakon nasarar lashe gasar da suka samu. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta nuna gwamnati ta cika wannan alƙawari ne bayan da…
Read More
‘Yan bindiga sun sace mutum 33 a Kachia, har da mace mai ciki

‘Yan bindiga sun sace mutum 33 a Kachia, har da mace mai ciki

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna aƙalla mutum guda ya mutu sannan an sace mutum 33 sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai a yankin ƙaramar hukumar Kachia da ke jihar. Harin wanda ya auku a Larabar da ta gabata da daddare a cikin Kachia, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama. Dakacin gundumar Kachia, Malam Idris Suleiman ya tabbatar da aukuwar harin a lokacin da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, tare da jami'an tsaro suka ziyarci yankin. Suleiman ya ce 'yan bindigar sun zo ne da yawansu da…
Read More
Juma’a Buhari zai tafi Landon a bisa dalilin duba lafiyarsa

Juma’a Buhari zai tafi Landon a bisa dalilin duba lafiyarsa

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai koma Landon ranar Juma'a kan batun da ya shafi kula da lafiyarsa. Sanarwar da mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Femi Adesina, ya fitar ta nuna bayan tafiyar, Buhari zai dawo gida Nijeriya ne a mako na biyu na watan gobe. Adesina ya ce,  “Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landon ran Juma'a, 25 ga Yuni, 2021 bisa dalili na duba lafiyarsa. “Sannan ya dawo a mako na biyu na Yuli, 2021".
Read More