06
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kansilan Guringawa a cikin Ƙaramar Hukumar Kumbotson Jihar Kano ya gabatar wa Babbar Sakatariyar Ilimi ta ƙaramar hukumar Kumbotso da ƙudurin sa na tallafa wa harkar ilimi daga tushe, kana ya gabatar mata da kwamitin da ya kafa na bunƙasa harkar ilimi a mazaɓar sa, wato 'Guringawa Ward Education Promotion Committee', inda kwamitin ya ƙunshi ƙwararrun malaman makarantun firamare, sakandare har zuwa jami'a, sannan da masu hannu da shuni da masu unguwanni da sauran jagororin al'umma har 11 a matsayin mambobin kwamitin. A Alhamis da ta gabata, kwana guda da kai ziyarar kansilan ofishin…