2023: Adamu ya yaba wa matsayin ƘungiyarƘwadago a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yaba wa Ƙungiyar Ƙwadogo ta Ƙasa reshen Jiihar Nasarawa dangane da tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakaninta da gwamnatin jihar saɓanin yadda lamarin yake a wasu jihohin ƙasar nan.

Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen wani gangame da ƙungiyar ƙwadagon a jihar ta shirya ta kuma gudanar a babban filin taro na Lafiya Square a jihar don nuna wa gwamnan jihar injiniya Abdullahi Sule cikakken goyon bayan mambobin ta baki ɗaya don bashi damar lashe zaɓen gwamnan na 2023 dake tafe.

Ya ce ba shakka qungiyar ƙwadago a jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamared Yusuf Iya ta cancanci yabo idan aka yi la’akari da cikakken haɗin kai da gudumawa da take bayarwa wajen cigaban ma’aikata da gwamnatin jihar a duka matakai.

Ya ce a kan haka ne ma ya sa a nata vangaren gwamnati nata ƙoƙari wajen cimma buƙatar ma’aikata a jihar.

Sanata Abdullahi Adamu ya ƙara da cewa wannan mataki da ƙungiyar ta ɗauka na gudanar da gangamin nuna goyon bayan ma’aikata wa gwamnan zai sa Jam’iyyar APC a jihar ta za ta cigaba da biya su hakokin su kamar yadda take yi musamman bayan zabukan 2023 dake tafe.

Shi ma da yake jawabi gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya gode wa namijin ƙoƙari da ƙungiyar kwadagon a jihar suka yi na bayyana wa duniya baki ɗaya cewa suna tare da shi a 2023 inda ya tabbatar musu cewa ba shakka hakan zai tilasta shi dole ya cigaba da biya musu buƙatar su da haƙƙoƙin su da suka haɗa da biyan albashi cikin lokaci da kuɗaɗen fensho ɗin su da alawus da ƙarin girma da sauran su.

Gwamnan ya kuma yi alƙawarin biya musu wasu sabbin buƙatun su da suka gabatar masa a yayin gangamin da suka haɗa da damar mallakar gidajen rukuni na gwamnatin jihar da wasu ma’aikatan gwamnatin ke ciki a yanzu da batun ƙarin girma da sauran su.

Tun farko a jawabin sa na maraba shugaban ƙungiyar ta ƙwadago a jihar Kwamared Yusuf Iya ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar gudanar da gangamin ne da nufin tabbatar wa gwamnan cikakken goyon bayan ma’aikata a jihar musamman bayan sun yi la’akari da hadin kai da kyakkyawar shugabanci da gwamnan ke gudanar a jihar kawo yanzu.

A cewarsa tun da gwamnan ya hau mulki ba ya ɓata lokaci wajen biyan su duka haƙƙoƙin su musamman waɗanda suka shafi jin daɗin su.

A kan haka nema ya sa a cewarsa ƙungiyar ta ga ya dace ta saka masa ta yin masa ruwan ƙuri’u a zaɓen na 2023.

Daga nan sai Kwamared Yusuf Iya ya kuma yi amfani da damar inda ya gabatar wa gwamnan da wasu ƙarin buƙatun ma’aikata a jihar da suka haɗa da gidaje da ƙarin girma da haƙƙin ‘yan fansho da sauransu.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *