2023: Na yi alƙawarin mayar da ‘yan Nijeriya miliyan 20 miloniya idan na zama shugaban ƙasa – Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya sha alwashin zai mayar da ‘yan Nijeriya mutum miliyan ashirin attajira muddin aka zaɓe shi ya zama shugaban Nijeriya a 2023.

Gwamna Bello ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bayyanar da ƙudirinsa na takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa wanda ya gudana a jiya Asabar a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Gwamnan ya bayan nazari mai zurfi ya gano cewa babu wanda ya cancanta da zama magajin Shugaba Muhammadu Buhari sai shi.

Ya ce Nijeriya na buƙatar matashi mai jini a jika a matsayin shugabanta domin ɗora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya wajen ci gaba da bai wa ƙasar irin kulawar da ta dace.

Ya ƙara da cewa, ya ishi ‘yan Nijeriya misali ganin irin kulawar da jiharsa ta Kogi ta samu a ƙarƙashin gwamnatinsa, wanda a cewarsa muddin aka ba shi wannan dama, zai yi wa ƙasa hidima ya gyara ta sama da yadda ya yi wa jihar Kogi hidima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *