2023: Osinbajo ya nesanta kansa da buɗe ofishin yaƙin neman zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ofishin yaƙin neman zaɓe da wasu masoyan mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo suka buɗe masa a Abuja.

Wasu da suke ikirarin magoya bayan mataimakin shugaban Nijeriya ne sun buɗe ofishin tallata shi domin ya tsaya takarar shugabancin ƙasar a shekara ta 2023.

Mutanen, waɗanda ke ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna The Progeressive Project, wato TPP a taƙaice, sun bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya cancanci shugabancin Nijeriya idan aka yi laakari da iliminsa da kuma ɗabiunsa.

Sakatariyar magoya bayan mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya tsaya takarar shuganbancin ƙasar a babban zave mai zuwa ba a ɓoye take ba, kasancewar an girka ta ne a ɗaya daga cikin unguwanni irin na alfarma a Abuja.

Ofishin bene ne mai hawa ɗaya, kuma a cikin harabar an girke hotunan mataimakin shugaban ƙasar wanda a jikin hotunan an yi rubutun da ke cewa shi ne ya cancanci jagorancin Nijeriya a zaɓen shekarar 2023.

Shugabannin ƙungiyar, sun bayyana cewa ɗabi`un mataimakin shugaban ƙasar ne suka ja hankalinsu wajen tallata shi a duniya. Alhaji Musa Gidaɗo shi ne sakataren ƙungiyar.

“Yadda ya ke bin shugaban ƙasa sau da ƙafa kuma shi ne kaɗai bai da bambanci tsakanin ko’ina a faɗin ƙasar, yana ganin kowa a matsayin ɗan Nijeriya, kuma mai ilimi ne ga hazaƙa, ga ƙoƙari da haƙuri, natsuwarsa mu ka gani cewa ya kamata mu sa shi a gaba ya zama shugaban ƙasa,” in ji shi.

Sai dai ƙungiyar ta yi ikirarin cewa babu wani da mataimakin shugaban ƙasa ya sani a cikin mambobinta kuma tana samun tallafi ne daga masoyansa da yawa.

Sai dai ɓangaren mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba shi da wata alaqa da waɗanda suka buɗe sabuwar sakatariyar.

Mai taimakawa shugaban ƙasa a kan harkokin ƙananan masana’antu a ofishin mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Abdurrahman Bappa Yola ya ce masoya Farfesa Yemi Osinbajo suka tara kuɗi domin buɗe masa ofis.

“Wannan abu ne wanda masoya ne kuma su ke ganin ya dace, ya cancanta su ke yi waɗannan abubuwa amma shi bai fito ya furta yana cikin wannan takara ba, kuma yana da maigida shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda babu wani abu da ke gabansa illa su ga sun sauke nauyin da al’umma su ka ɗora mu su,” in ji shi.

Duk da cewa ɓangaren mataimakin shugaban ƙasar ya nuna ba shi da nasaba da ƙungiyar magoya bayan nasa, masana harkokin siyasa a ɓangare guda na fassara ɓullar irin wannan gangami na magoya baya da cewa wani salo ne na bugun juji domin a ji ƙarar gwazarma, wato maauni ne na irin tagomashin ɗan siyasa a wajen iyayen gidansu da kuma sauran jamaa.

Tuni dai su ma magoya bayan jigo a jam`iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, wanda ubangidan siyasar mataimakin shugaban ƙasar ne, sun ƙaddamar da nasu ofishin na goyon bayan ya tsaya takarar shugabancin Nijeriyar. Ko da yake bai fito fili ya ce zai tsaya ba.

A yanzu `yan Nijeriya sun zuba ido su ga yadda wannan zarwarcin mulkin ƙasar zai kaya tsakani ɗa da uba amma irin na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *