An kashe ‘yan sanda 7 a hare-haren Rivers

Daga UMAR M. GOMBE

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Rivers ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta su bakwai sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar. Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Nnamdi Omoni, shi ne ya tabbatar da hakan

A cewar jami’in, “Maharan sun kashe jami’ansu biyu a shingen binciken abubuwan hawa a ƙauyen Choba da ke tsakanin ƙaramar hukumar Obio/Akpor da ƙaramar hukumar Emohua, sannan suka banka wa wata mota mallakar ɗaya daga cikin jami’an da lamarin ya shafa.”

Kazalika, ya ce ‘yan bindigar sun sake kai wa ofishin ‘yan sanda hari a garin Rumuji a ƙaramar hukumar Emohua, a nan ma sun hallaka wasu ‘yan sanda tare da ƙona musu motar aiki.

Rundunar ta ce ‘yan bindigar sun far wa ofishinta da ke Elimgbu a yankin ƙaramar hukumar Obio/Akpor inda a nan ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu.

SP Omoni ya ce an yi ɗauki ba daɗi tsakanin jami’ansu da ‘yan bindigar wanda a cewarsa, da alama ‘yan bindigar ba su ji da daɗi ba.

Haka nan, ya bada tabbcin yayin hare-haren babu ofishin ‘yan sanda ko guda da aka ƙona, sai dai ‘yan bindigar sun tsere da wasu bindigogi.

Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Friday Eboka, ya bada umarnin a gudanar bincike mai zurfi kan lamarin.

Duk da dai ba kai ga bayyana ko su wane ne maharan ba, amma akwai zargi mai karfi da ke nuni da cewa ‘yan tsagerun IPOB ne suka kai hare-haren