NDLEA ta cafke masu fataucin miyagun ƙwayoyi 363 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Hukumar Hana Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen jahar jigawa, ta sami nasarar kama masu shaye-shaye mutun 363 a faɗin jahar.

Kwamandar hukumar a jihar Jigawa, Hania Maryam Gambo Sani, ita ce ta tabbatar faruwar hakan, inda ta ce sun cafke masu laifin ne tsakanin Yulin shekarar da ta gabata zuwa 15 ga Yunin 2021.

Maryam ta bayyana haka ne awani taron manema labarai da ta kira a ranar Asabar da ta gabata a matsayin wani ɓangare na abikin ranar hana shan miyagun ƙwayoyi ta duniya da aka gabatar a Dutse, babban birnin jihar.

Daga nan, Maryam ta nuna damuwarta game da yawaitar masu shaye-shayen
miyagun ƙwayoyi a jahar Jigawa musamman ma a tsakanin matasa.

Ta ce adadin kayan maye da matasa masu shaye-shayen da suka kama a jihar a bana ya zarce wanda suka kama a shekarun baya.

Don haka ne ta shawarci iyaye da su matse ƙaimi wajen sanya wa ‘ya’yansu ido don hana su ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Jami’ar ta alaƙanta yawaitar shaye-shaye a tsakanin matasa da ɓullar cutar korona wanda a dalilin haka aka kafa dokar kulle wanda hakan ya yi tasiri wajen talauta mutane da kuma haifar da rashin aiki.