AIB ta yi ƙarin haske kan binciken haɗarin jirgin saman da ya ci ran Attahiru da wasu

Daga WAKILINMU

Hukumar Binciken Haɗurra (AIB) ta ba da sanarwar cewa nan da mako guda za ta fitar sakamakon binciken farko dangane da haɗarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Rundunar Sojoji , Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, tare da wasu mutum 10.

Babban Jami’in Hukumar, Akin Olateru, shi ne ya bayyana hakan ran Alhamis da ta gabata a Abuja yayin da yake bayyana rahotannin da hukumar ta shirya kan haɗurran jirgin sama da suka auku har guda takwas.

Sai dai, jami’in ya ce bayan miƙa rahoton nasu, zaɓi ya rage ga Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya (NAF), ko ta bayyana wa ‘yan ƙasa abin da rahoton ya ƙunsa ko kuma ta bar wa kanta, sabida a cewarsa hukumar AIB ba ta da hurumin bayyanar da abin da rahoton ya ƙunsa ga duniya.

Tun bayan aukuwar haɗarin ne NAF ta buƙaci AIB ta jagoranci bincike kan aukuwar haɗarin.

Da yake amsa tambaya kan abin da ya haifar da jinkiri wajen fitar da rahoton haɗarin jirgin, Olateru ya ce, “Bincike irin wannan na ɗaukar lokaci aƙalla watanni 18. Kuma haɗarin da ake magana a kai ya shafi jirgin NAF, amma kuma ya auku ne a filin jirgin farar hula.

“Wannan ya sa NAF ta ga cewa akwai rawar da za mu taka wajen taya ta gudanar da bincike kan haɗarin wanda ake kan gudanarwa a yanzu.”