WAƘA: Barka da Salla

Daga NASIRU G. AHMAD

Barka da salla ‘yan uwa,
Allah ya ba mu amintuwa.

Mun yi ibadar azumi,
Na wata guda ba yankuwa.

Mun bar abinci da shan ruwa,
Ga Ilahu don mu kusantuwa.

Zikiri na Allah mun ta yi,
Ƙur’ani mun yi karantuwa.

Nafilfilu a cikin dare,
Don hasanarmu ta ƙaruwa.

Zakka ta Kono mun fitar,
Mun ba wa masu buƙatuwa.

Salla ta Idi mun zuwa,
A cikin ado da nishaɗuwa.

Mun ɗebi girki ba nawa,
Murnarmu ba ta misaltuwa.

Duk wanga baiwa ce daga,
Allah da ta ci a goduwa.

Wasunmu an fara da su,
Sun tafi ba ran komuwa.

Wasunmu na kwance gida,
Da asibbiti ba waluwa.

Sun so a yo murnar da su,
Cuta ga su tai hanuwa.

Ƙalubale da yake ga mu,
Ga Rabbi mui ta shukurtuwa.

Kyawu na aiki kar mu bar,
Kullum ya rinƙa gudanuwa.

Zumunci mui sadar da shi,
Domin mu zam daɗa shaƙuwa.

Domin idan tafiya ta zo,
Mu san abin yin riƙuwa.

Ya Rabbi sa dukkan iba-
dojinmu gunka su karɓuwa.

Ka jiqan waɗanda sun tafi,
A cikin watan ka yi afuwa.

Dukkan marassa lafiya,
Sa lafiyarsu ta komuwa.

Mu ma ka sanya lafiya,
A gare mu tai ingantawa.

Ya ‘yan uwa nai gaisuwa,
A gare ku mai yin ƙamsuwa.

Barka da salla ƙarama,
Ga maza da mata na yiwa.

Allah ya maimaita mana,
Ta baɗin baɗi ba yankuwa.

Mu zamo da ƙoshin lafiya,
Domin ga Rabbi mu bautuwa.

Darajar Rasulu abin biya,
Ya zamo da mu zai cetuwa.

Nasiru G. Ahmad nake,
Mai son ku babu nifaƙuwa.