Mahara sun matsa lamba

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Mahara a sassan Nijeriya na kara matsa lamba ko ƙaimi kan hare-hare don jefa tsoro da nuna gazawar tsarin da zai iya ƙalubalantarsu. Maharan a dazuka da birane na barazana ga rayuwar jama’a da kawo zaman zullumi. Gabanin ɓullowar ɓarayin daji, an samu wani yanayi ne inda a Abuja ma a kan kai hari da bom da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gaskiya wasu hare-haren na da ban mamaki yadda su ke faruwa. Ko ma waye ya ke alhakin kai harin, rashin imanin sa ya kai a rubuta a jikin dutse.

Harin bom ’yar gaba ɗaya ne ga yara da manya, jami’in tsaro da kowa ma. Ko a madakatar mota wasu kan iya tada bam don kashe mutanen da ba su yi mu su laifin komai ba. Kukan kura da ‘yan ta’adda su ka yi su ka kai farmaki gidan yarin Kuje ya kawo damuwa ainun. Tuni dai wasu qasurguman masu laifi da ke gidan yarin su ka arce inda hakan ke nuna akwai barazana ga rayuwar sauran jama’a matuƙar ba a kamo waɗannan mutanen ba.

Harin ya nuna wasu miyagun iri sun ɗauki azamar ƙwato mutanensu da ke kulle a gidan wa imma waɗanda a ka yanke wa hukunci ko waɗanda ke jiran hukunci. Garin Kuje ya shiga cikin firgici lokacin wannan hari don rugugin harbe-harbe da ruwan wuta inda a ka ba da labarin ganin waɗanda ke gidan na sulalewa don tsira daga riƙe su da hukuma ta yi. Kazalika jami’an tsaron gidan yarin ma sun shiga yanayi na yaƙi da tunkarar mutanen da su ka zo mu su da ƙarfin tsiya da wannan ke nuna dole a fito a fuskance su ko ma yaya sakamakon zai kasance. Wani abun tsoron ma shi ne albarushi da kan iya batan kai ya samu wanda ke cikin gidan sa ko ya na barci ko ya rakube.

Dole a nuna matuƙar damuwa da afkuwar wannan akasin kasancewar wannan gidan yarin na ɗauke da gaggan masu laifi da ma wasu ‘yan siyasa da a ka ajiye da tuhuma ko hukuncin yin zarmiya. Irin wannan hari kan iya shafar waɗanda su ka rungumi ƙaddara ma cikin waɗanda a ka yankewa hukunci, sun zauna su na jiran kammalar wa’adinsu. Kun ga irin waɗannan ma’abota gidan yarin za su shiga damuwa da jin rugugin harbe-harbe don komai ma ka iya faruwa.

Duk wanda ya arce daga gidan yari zai iya duk duk wani matakin tsira ko da hakan zai kai ga samar da rauni ko ma hallaka rai don cimma wannan buri. Ba a kan gidan yarin Kuje kaɗai a ka kai irin wannan harin ba, miyagu sun kai hari a gidajen yari da dama da su ka haɗa da na Jos a jihar Filato, Kogi, Oyo, Benin da sauran su. A duk lokacin kai hare-haren a kan yi barin wuta inda kuma na gidan yari kan nemi arcewa duk da labarum daga bisani a kan kamo wasu daga cikin su don sake tsare su. Jami’an tsaron gidajen yari kan rasa ran su a wannan muhimmin aiki da su ke gudanarwa na kula da tsare miyagun iri. Don haka wannan ya nuna akwai buƙatar ɗaukar matakan da su ka dace don kare gidajen yari daga hare-hare.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya samu lokaci inda ya ziyarci gidan yarin don gane idon sa abun da ya faru. Zuwan shugaban na da muhimmanci don zai yiwu a samu saukin ɗaukar kwararan matakan kare gidajen yarin. Gwamnatin shugaba Buhari ta sauya sunan gidajen yari zuwa gidajen gyaran hali. Don haka ai abu ne mai muhimmanci a dau duk matakin da ya kamata wajen kare gidan gyaran hali da a ke sa ran kan sauya ɗabi’ar mugayen mutane zuwa halin kirki.

Ɗan gidan yari na zaune a na gyara ma sa hali sai kwatsam a ji ƙarar harbe-harbe na wasu da ke son fitar da mutanen su daga gidan yarin. Akwai labaran da mu ka samu cewa duk da yawan waɗanda su ka arce daga gidan yarin na Kuje an samu wasu na zaune a gidan kuma dama irin mutanen indai labarin ya tabbata ba alamun za su biyewa ’yan ta’adda wajen guduwa don ba sa buƙatar hakan. Kuma abun gode wa Allah ne in an samu mutanen da su ka yi bakam su ka zauna ba abun da ya same su.

Hakanan da fatan ba su shiga firgici ba da zai iya taba kwakwalwarsu da haƙiƙa ta ke cikin damuwa in an duba an rufe ko tsare su a yanayin rayuwar da ba su saba da ita ba. Ba za a yi tantama ba in likitoci sun shiga gidan yarin don duba lafiyar waɗanda ba su gudu ba ko ta kai a ɗauko wasu a kai asibiti don kulawa ta musamman. Kuma a fahimci cewa Kuje na nan daf da mashigar babban filin saukar jiragen sama na Abuja wato Nnamdi Azikwe da dare da rana baki daga ciki da wajen Nijeriya ke karakaina a wajen.

Haqiqa ba da irin waɗannan labaru ta hanya mai tsauri ka iya sanya wanda bai san Nijeriya ba sosai ko Abuja ya yi shakkar shigowa ta hanyar filin jirgin. Irin wannan akasi ke sanya masu son shigowa daga waje kan yi ɗari-ɗari da zuwa ƙasa. Ba gwamnatin da ta ke da azamar kare qasa da za ta so irin waɗannan dalilai su firgita ’yan gida ma bare waɗanda su ke baki.

Wani abun da ke damuna ma shi ne yanda za ka ga baki na kaffa-kaffa da yawo hatta a wasu sassan babban birnin taraiya Abuja. Afkuwar wannan akasi da ya nuna miyagu sun arce daga gidan yarin Kuje zai kara firgita mutane su ƙara takatsantsan. Rashin walwalar jama’a kuma kai tsaye zai shafi rayuwar yau da kullum da zai iya illata tattalin arziki da kai tsaye kuma zai kara tsananta kuncin talauci, takaici da baƙin ciki. Zama cikin salama da barci da ido biyu a rufe na kawo cigaban ƙasa. Garuruwa da dama a Nijeriya na kwana cikin firgici. Birane ba lafiya ƙauyuka ba lafiya kai gonaki ko dazuka ma ba lafiya.

Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya buƙaci basaraken Kuje GOMO na Kuje Haruna Tanko Jibrin ya haɗa kai da jama’ar sa da kuma jami’an tsaro don cafko waɗanda su ka arce daga gidan yarin Kuje.

Minista Bello na magana ne a ziyarar gani da ido gidan yarin bayan harin ‘yan bindiga inda fursunoni da sauran su da dama su ka arce. Tuni ma ministan tsaro Janar Bashir Magashi ya tabbatar da arcewar mazauna gidan yari da dama. Majiya ta nuna gidan yarin Kuje na ɗauke da ’yan Boko Haram 64 inda 60 su ka arce. Daga bisani an ga faifan bidiyon da a ka ce daga ISWAP ne na ɗaukar alhakin wannan harin.

Ministan ya ce, ba zai yiwu mai laifi ya shiga cikin jama’a ya saje da su ba don haka za a iya kamo mutanen a duk inda su ka ɓuya.

Musa Bello bai tsaya a nan ba sai da ya ambaci abun da a ke tsammani daga kalaman mutum irin sa shi ne ba da tabbacin inganta tsaro a gidan yarin da kewaye.

Ta ziyarar ministan an fahimci cewa ɗaya daga jami’an tsaron kare farar hula da ke aiki a gidan yarin ya rasa ransa. Musa Bello ya miƙa ta’aziyya ga wannan rashin. Kuma hakan ya nuna akwai jami’an tsaro na ɓangarori daban-daban da ke kula da tsaron gidan yarin. Duk da yawancin mu bam asana tsaro ba ne amma za mu ce kamar akwai ƙarancin amfani da labarun sirri wajen yaƙi ko hana afkuwar irin wannan mummunan hari. Ko da ya ke na ji wani babban jami’in ’yan sanda na Abuja na nuna in ka ga an samu wata matsalar tsaro to tamkar ɗaya ne cikin da yawa da a ka kwance damarar afkuwarsu. Shi kan sa minista Bello ya ƙarfafa irin wannan bayani.

In mun ɗauki bayanan jami’ai da mahukuntan Abuja, za mu tafi a kan harin da a ka kai kan gidan yarin Kuje ɗaya ne daha hare-hare da dama da ba mamaki in an hana afkuwar wasu daga ciki ko a baya an tava kawar da wani hari kan gidan yarin. Mu na fata cewa wannan alwashi na ɗaukar karin matakan tsaro kan gidan yarin da gewaye zai tabbata ya zama irin wannan bai sake faruwa ba a nan gaba. Don a gaskiya matuƙar irin waɗannan hare-hare za su cigaba da faruwa, masu ƙananan laifuka da akan kai gidan yari ko wasu manyan mutanen ƙasa za su shiga firgicin tsira da ran su gabanin samun kan su daga wannan yanayi na tuhuma ko jiran wa’adin fita ko wani matakin daban.

Kammalawa;

Kamar yadda shugaba Buhari ya kia ziyara gidan yari da kuma akasin ya zo a rana ko lokaci ɗaya da fafatawar da kwambar motocin sa su ka yi da ’yan bindiga a Katsina, ya nuna farkarwa ce ta buƙatar sauya dabaru da ba da sabbin umurni na kakkarfar tsari da zai kawo salama a qasa. Haƙiƙa in a ka yi sake lamarin taɓarɓarewar tsaron nan fa zai iya shiga inda ba a tsammani.