Atiku ko Tinubu: Wanne ba wanne ba?

Daga RAHMA ABDULMAJID

Eh! Akan yan takararmu guda biyu waɗanda da alamar su ne za su fafata da gaske a kan kujerar shugaban ƙasa. Alhaji Atiku Abubakar ɗan Shekaru 76 (wataƙil da takwas) da Alhaji Ahmad Bola Tinubu dan shekaru 70 (wataƙil 78).

Ga duk mai kallon wasan kwaikwayo mai dogon zango, ya san munin ƙarshe. Hakazalika, mai kallon ƙwallon ƙafa ya san bugun fanareti a wasan ƙarshe.

To a siyasar waɗannan mutanen ma da alamar za mu san wasan ƙarshe, domin  ko za su buga wasan ƙarshe inda a wannan karon dolen dole ne ɗaya ya yi wa ɗaya ritaya.

Ba mu san dalilin da ya sa Allah Ya zaɓi abokan kuma masana tuggun junan su kara da juna a wannan wasan ba. Amma Ko ma menene dalili, ina tabbatar muku da wasan zai yi kafirin daɗi.

Domin za a zuba masa sinadaran naci, kuɗi, tsufa, karɓuwa da sanya Jamiyya a aljihu.

Bari mu kalli damammakin da kowanne ke da su da kuma zai iya amfani da su kai tsaye, Da kuma manyan ƙalubalen da ka iya kawo masa tsaiko.

Atiku ya fi Tinubu damammaki da suka haɗa fitowa daga yankin da ake da tsantsar ƙuri’a, bai da barazanar faɗawa rikicin tikitin musulmi da musulmi; amma bai da ƙasurgumar gwamnati da za ta dafa wa nasararsa baya kamar Tinubu me gwamnoni 22,  da Shugaban ƙasa, Shugaban Majalisar dattijai,  shugaban Majalisar wakilai da uwa uba tutar jam’iyya mai mulki da ta lashi takobin sai ta shekara aƙalla 16 irin na PDP.

Tinubu ya fi Atiku tarihin nasara a zaɓe. Tunda baya faɗuwa zaɓe, yan takarasa na gaske ba sa faɗuwa, ba kamar Atiku da tun bayan tikitin mataimakin shugaban ƙasa bai sake cin zaɓe ba.

Haka ma a ƙwarewa wajen gudanar da mulki tunda har yau Atiku bai yi wata rawar kirki an gani ba. Baya da zama mataimaki shugaban ƙasa wanda duk aikin da aka yi a lokacin Obasanjo ke ɗaukar ladarsa, saɓanin Jagoran na Eko Oni Baje.

Wanda da ya riqe Jaha shekara biyar ba tare da tallafin gwamnatin tarayya ba, kuma ya tara kuɗin manyan aiyukanta daga biliyan 14 zuwa 240,  Sannan Tinubu ya fito daga yankin da ba ɗan takara ne kawai yake da naci ba kusan duk yankin kowa naci ne da shi.

Kuma sun yi imani da cewa yanzu lokacinsu ne ‘yan Arewa sun gama nasu zangon mulkin shi ya sa ma ake kiran takararsu da (Emi Lokan) wato lokacina ne.

Kuma da alamar wannan zance nawa har ‘yan Arewa ya yi wa tasiri, sai dai Tinubu ko kaɗan ba shi da lafiyar Atiku. Sannan yadda rashin lafiyar ke taazzara tana fitowa ko ba ta yi komai ba, za ta bayyana a yawon yaqin neman zaɓe kamar yadda ta bayyana a bidiyo da uke ta yawo.

A wani waje ma an ga sam ya kasa riqe tutar da ya kusa kashe kansa don ya samo ta. Ga duk ɗan Nijeriya da  ya rayu daga shekarar 2003 zuwa yau ya san halin da marasa lafiya suka jefa ƙasar nan da har yau ba mu fita ba.

To zai yi shakkar tunkarar akwatin zaɓe da niyyar jefa wa Tinubu, Idan har tsufa da rashin lafiyar Shugaba Buhari sun lalata Nijeriya, ina kuma ga mutumin da ko tuta baya iya riƙewa sai da taimakon hannun Buhari? Kenan dai duk fitar da Tinubu zai yi ya nemi quri’a to fa sai ya yi wa Atiku kamfe da rashin lafiyarsa ko yana so ko baya so

Inda ‘yan takarar biyu suka yi kamanceceniya:

Atiku na da Jama’a da ƙaton yanki, Tinubu na da jama’a da gwamnati.
Atiku Musulmi ne, Tinubu Musulmi ne.

Atiku na da kuɗi na masifa, Tinubu na da kuɗi na masifa. 

Atiku ya iya almubazzaranci a kan  ƙuri’a, Tinubu ya iya watanda a kan ƙuri’ar wani ma balle tasa.

Atiku ya tava neman taimakon Tinubu a zamanin Obasanjo, Tinubu ya taɓa neman taimakon Atiku a kan ɗora Buhari.

Atiku ya sa jam’iyyarsa a aljihu, Tinubu ya sa ‘ya’yan jam’iyyar a aljihu.

Atiku na da sanya Iyali a cikin mulki, ko da yake mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi, fesledi biyu aka yi: da Titi da Marigayiya Stella, Tinubu kuwa tuni ‘My darling wife’ na cikin mulkin ma, don sanata ce.

Atiku da Tinubu na ɓoye wa jama’a bayanai a kan arzikinsu wanda ake zargin duk na ƙasa ne da suka wawushe, suke riritawa har shekaru uku.

Da me talaka zai tsira?

Mu dai talakawa da alamar Allah Ya kaddara mana:
1 Musulmi na iya sake mulkar mu aƙalla na shekara 4.

2 Ta ko’ina za a iya samun kuɗin cinikin ƙuri’armu, sai buhunhunan shinkafa. 

  1. Ƙwararru za su shugabance mu ko da ba su da lafiya, amma ƙwarewarsu da alamar tana musu tasiri, za a ga haka a yadda suka ƙwato tikitin takara ba tare da gudunmuwar kowace gwamnati ba.
  2. Za mu sallami tsaffin nan biyu mu huta.
  3. Allah zai mana zaɓi na alheri a cikinsu idan muka dage da addu’a da hana kanmu zaɓen su saboda abinda z amu samu, ba don cigaban Najeriya ba. Allah ya yi man zavin alkhairi.

Rahma Abdulmajid marubuciyar ce kuma manazarciya a kan al’amuran yau da kullum. Ta rubuto daga Abuja.