Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano ya nemi haɗin kan Hukumar Kwastam da SSS a jihar

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

A ranar Larabar wannan makon ne Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawal ya kai wa takwarorinsa na hukumar hana fasa ƙwauri mai kula da shiyyar Kano da Jigawa da kuma hukumar farin kaya wato SSS ziyarar aiki, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kano SP Haruna Abdullah Kiyawa ya fitar ga manema labarai.

Da yake jawabi yayin ganawa da shugabannin hukumomin biyu, CP Abubakar Lawal Daura ya ce ya ziyarci vangarorin guda biyu ne don gabatar da kansa tare da neman goyon bayan wannan hukumomi don samun nasarar aiki tare da samar da kyakkyawan tsaro a jihar kano.

Shi ma a nasa jawabin lokacin da ya karɓi kwamishinan kwantrolan hukumar mai kula da shiyyar Kano da Jigawa Coln, Mu’azu Hassan Raji, ya yi wa kwamishinan barka da zuwa da sauran tawagarsa, inda yaka dacewa kasancewar jin iri ƙoƙarin kwamishinan da yake yana ganin akwai damar koyi daga gare shi don haka babu wata hukumar tsaro da za ta yi aiki ta samu nasara ba tare da hukumar ‘yan sanda ba, dalon haka za su yi duk mai yuwuwa don haɗa gwuiwa su maida Kano kan turbar mun tsira.

Kazalika shi ma da yake karɓar kwamishinan yayin ziyarar shugaban hukumar ta farin kaya na jihar Kano Alhaji Hassan N. Mohammed ya yi matuƙar godiya da wannan ziyarar aiki da shugaban hukumar ta ‘yan sanda na Kano ya kawo masu, don haka matsayinsu na jami’an sirri suna taka muhimmiyar rawa tare da da jami’an ‘yan sanda da suke kan gaba wajen bada cikakken bayanin sirri, Hassan ya ce lallai za su cigaba da ba hukumar ‘yan sanda goyon baya da aiki tare don samun nasara.