Shugaban matan PDP na Zamfara ta koma APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Shugabar matan jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara, Hajiya Madina Shehu ta fice daga jam’iyyar ta koma jam’iyya mai mulki a jihar, APC.

Ta bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ta yi da Gwamna Matawalle a ranar Alhamis.

A cewarta, ta bar jam’iyyar ne saboda rashin shugabanci nagari da rikon amana.

“Na yanke shawarar barin jam’iyyata ta PDP tare da shugabannin mata daga dukkan ƙananan hukumomin jihar 14 muka koma jam’iyyar APC mai mulki saboda PDP a Zamfara ba ta da salon shugabanci,” inji ta.

Gwamna Matawalle a nasa ɓangaren ya bayyana sauya shekar Hajiya Madina Shehu da mambobinta a matsayin abin maraba da ci gaban Jamiyyar APC a zaɓe mai karatowa.

“Muna sa ran ƙarin masu sauya sheƙa zuwa APC daga PDP a jihar masu ɗimbin yawa,” inji Gwamna Matawalle.

Matawalle ya yi alƙawarin ɗaukar dukkanin mambobin Jamiyyar APC a jihar a matsayin halastattun ‘yan jamiyya tare da aiki da su domin samun nasarar APC a 2023 a jihar.

Ya kuma buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da shugabannin jam’iyyar a jihar da su kasance masu haɗin kai da bin doka da oda domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa a jihar.