Shugaban marasa rinjaye na majalisar Kano da ‘yan dabar siyasa 160 sun faɗa komar ‘yan sanda

Daga RABI’U SANUSI a Kano.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano kuma ɗan takarar kujerar majalisar jihar ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Hon. Isyaku Ali Danja da wasu ‘yan dabar siyasa sama da 161 sun faɗa komar ‘yan sanda a jihar Kano.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da Kwamishinan’Yan ‘Yan Sandan jihar mai kula da harkokin zaɓe, CP Usaini Mohammed Gumel, yake gabatar wa manema labarai waɗanda ake zargi da hannu wajen abin da ya bayyana da cin amanar ƙasa.

Gumel ya ce rundunar da sauran takwarorinta a jihar sun samu nasarar kama waɗanda ake zargi da tada zaune tsaye tare da ƙoƙarin ƙona ofishin ‘yan sanda dake ƙaramar hukumar Gezawa da na hukumar zaɓe a wannan yankin.

Ya ce sun kuma samu nasarar yin awon gaba da wasu da ake zargin su da hannu wajen siyen ƙuri’a a yayin gudanar da zaɓen tare da hargitsa rumfunan zaɓe yayin da ake gudanar da zaɓen.

Kazalika, Kwamishinan ya tabbatar da ba lauyoyin hukumar dama da masu gabatar da ƙara da kuma ƙwararrun masu bincike don duba ainahin abin da aka yi a wancan harin da aka yi yunƙurin kaiwa ofishin ‘yan sandan na ƙaramar hukumar ta Gezawa dan gudanar da bincike kamar yadda Shugaban ‘Yan Sanda na Ƙasa ya ba da umarni.

Daga nan, Kwamishinan ya ƙara miƙa godiyarsa bisa ga kayan aikin da hedikwatar ta aike wa rundunar ta Kano dan gudanar da aiki yadda ya kamata.

Daga ƙarshe, ya gargaɗi al’ummar jihar Kano da su guji yaɗa labaran da ba su da tushe ko kalaman ɓatanci da zai iya kawo wa jihar koma baya, ya kuma buƙaci ƙara fahimtar hana wani taron murnar lashe zaɓe ko makamancin hakan a faɗin jihar.