Amfani da hikima a wa’azin gyara kayanka

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kawo yanzu dai ƙurar da ta tashi biyo bayan sauke fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, daga limanci da karantarwa a masallacin ’yan majalisar ƙasa da ke unguwar Apo ta lafa, duk kuwa da yadda ’yan Nijeriya suka riƙa yi wa matakin da kwamitin gudanarwar masallacin ya ɗauka na sauke babban malamin, tofin Allah tsine. Saboda ganin kuskuren yin haka, da kuma ra’ayin goyon bayan kalaman da malamin ya yi amfani da su cikin huɗubar da ya gabatar a masallacin, Juma’ar da ta gabata.

Maganganun da suka riƙa yawo a zaurukan sada zumunta da kafofin watsa labarai tsakanin shugaban kwamitin masallacin Sanata Sa’idu Muhammad Ɗan Sadau, Sheikh Nuru Khalid da magoya baya daga kowanne vangare, daga dakatarwar farko da aka yi wa malamin zuwa saukewa ta gaba ɗaya, ba masu daɗin saurare ba ne, kuma alamu ne da ke nuni da cewa lallai za a iya fuskantar babban ƙalubale nan gaba, yayin da Babban Zaɓen 2023 ya ke ƙara gabatowa, wajen amfani da cibiyoyin addini don wasa da zukatan ’yan Nijeriya. Duk kuwa da haɗarin da hakan ke da shi ga zaman lafiya da tsaro a ƙasar nan.

Idan za ku iya tunawa ko a makonni biyu da suka gabata, wannan shafi ya yi tsokaci kan wannan matsala, ƙarƙashin taken ‘Haɗarin Shigar Da Addini Cikin Siyasa’ inda na ja hankalin ’yan Nijeriya su kaucewa amfani da masallatai da majami’u ana yaɗa manufofin siyasa, sukar gwamnati, ko kuma kare muradun wani ɗan takara da sunan addini. Saboda illar da hakan za ta haifar a gaba. Tun ba a je da nisa ba ga alamu nan sun fara bayyana cewa, idan ba a yi aiki da hankali yadda ya kamata ba, babu shakka za a samu damuwa.

Har wa yau, a wani rubutu da na yi a wannan shafi cikin watan Satumba na shekarar da ta gabata, mai taken ‘Ya Kamata Malamai Su Riƙa Yi Wa Bakin Su Linzami’ nan ma na ja hankalin malamai, fastoci da masu wa’azi su riqa tausasa harshen su wajen isar da saqonnin su na huɗubobi ga magoya bayansu ta yadda ba zai riqa nuna alamu na tunzurawa ko cusa ƙyamar gwamnati ko wani addini a zukatan ’yan Nijeriya ba.

Ana samun wasu masu iƙirarin cewa su mutanen Allah ne, masu gaskiya ne, da tarin ilimi, amma ayyukan su da kalaman su yana nuna akasin haka. Yayin da sau da dama suke amfani da inda ra’ayin mafi akasarin jama’a, musamman mabiyansu, ya karkata ne ko abin da ya fi ɗaukar hankalin ’yan ƙasa, su bayyana tasu fahimtar da za a ɗauka a matsayin ita ce daidai ko ita ce ta dace da bin Allah, ko da kuwa akwai kuskuren fahimta ko son zuciya da ra’ayi a kai. 

Bai kamata a samu malamin addini, fasto ko Rabaran yana ƙoƙarin yaɗa saƙonnin qiyayya ko raba kan jama’a ba, domin suna da saɓanin fahimta a keɓance ko a ƙungiyance da wasu ba. Ko kuma a samu malami dumu dumu cikin maganganu irin na adawa da gwamnati, ko tozarta wasu ma’abota addini ko masu faɗa a ji, ko zuga magoya baya ƙin yin biyayya ga wasu manufofin gwamnati ko abin da ya shafi tsaro, kiwon lafiya ko zaman tare tsakanin addinai da ƙabilu mabambanta. Hakan yana da haɗari sosai ga al’amarin zamantakewa, da mutuncin su kansu malaman da kimar su a cikin al’umma. 

Mun sha ganin inda malami da ke taƙama da gadara da magoya baya ke ganin ya fi ƙarfin doka ko gwamnati, a ƙarshe ya zama abin kyara da tsangwama, daga ɓangarori daban-daban. Mun ga inda alaƙa da ’yan siyasa ta jefa wasu malamai da ake ganin su da kima da martaba, cikin zargin cin kuɗin makamai da sauran su. Taurin kan wasu malamai saboda ganin yawan magoya baya ya jefa ƙasa cikin ruɗanin siyasa da tsaro, wanda har yanzu ake kokawa da shi. 

Mun sha ji da ganin yadda wasu masu wa’azi da suke yaɗa maganganu na tunzurawa da ƙyamar wani ɓangaren al’umma, sakamakon bambancin addini, ɓangaranci, siyasa, ko qabila. Yadda za ka ga mai wa’azi ya dage yana gayawa mabiyansa ko almajiransa wasu abubuwa da sam ba daidai ba ne, ko kuma sun saɓa wa hankali da bincike na masana. Amma zai yi amfani da tasirinsa a wajen su, ya nuna musu cewa, abin da ake ƙoƙarin ɗora ’yan qasa a kai ba daidai ba ne, wani makirci ne ko yaudara ce don a cutar da su, saboda a nisanta su da addini ko gurɓata makomar su. Ko kuma kalamai irin na ’yan adawa, ko da kuwa mahangarsu a siyasance ba iri ɗaya ba ce, amma kamanceceniya wajen salo da lokacin furzar da maganganun sai su zama daidai da na masu adawar siyasa da gwamnati, a haka kuma za a kalle shi. 

Salon nuna izza da gadara, ko kambamawa cikin kalaman da ake amfani da su yana nuna girman riqa da tumbatsar da wasu malamai ke ganin sun yi, tare da riya cewa babu abin da zai faru da su, saboda goyon bayan da suke samu daga wajen mabiyansu ko wasu ’yan Nijeriya masu irin tunanin su, kuskure mai girma. Domin kuwa babu wanda matsayin sa ya fi na martabar ƙasa da zaman lafiyar ta. Komai shaharar malami ko yawan mabiyansa ko tarin ilimin sa da furfurarsa, matuƙar karantarwarsa za ta zama barazana ga zaman lafiya da tsaro tilas ne a yi masa linzami.

Ba na goyon bayan cin zarafin malami ko jagoran addini, ko kuma ɗaukar matakin tauyewa wani ɗan ƙasa ’yancin sa na faɗin albarkacin baki. Amma ya kamata dukkan mu mu sani cewa, inda ’yancin mu ya tsaya a nan na wasu nasu ya ke farawa. Kuma dole ne mu sa a ran mu cewa, dokar ƙasa da martabar hukuma su ne sama da kowa, a kowacce ƙasa ta duniya.

A nan ba ina nufin goyon bayan matakin da kwamitin masallacin ’yan majalisar ƙasa na Apo suka ɗauka kan Sheikh Nuru Khalid ko kuma sukar wa’azin da ya gabatar da a ciki ya shawarci ’yan Nijeriya su ƙaurace wa zaɓe matuƙar ba a shawo kan ƙalubalen tsaro da asarar rayuka da ake fama da shi a ƙasar nan ba ne. Amma manufar rubutuna na yau shi ne, malamai da fastoci da duk wani alamin addini, su zama masu taka tsantsan da hattara cikin maganganun su, saboda halin da ’yan Nijeriya ke ciki kowa a kusa ya ke, wasu kalaman da ake ganin ba komai ba ne ko kuma gaskiya ake faɗa, suna iya zama sanadin aukuwar wani tunzuri da ba zai yi wa kowa daɗi ba.

Ba zai yiwu a raba malami ko fasto da ra’ayin sa na siyasa ko wata mahanga da aƙidar da yake ganin ita ce mafi dacewa a yi riƙo da ita ba, saboda da shi ma mutum ne kuma ɗan ƙasa. Amma ra’ayi ko son zuciyar sa bai kamata ya saɓa wa tsarin dokokin ƙasa ko fita daga hurumin addini ba. Ya kamata cibiyoyin addini su zama wurare ne na tarbiyyar ruhin jama’a, gyaran hali, da kusantar da su zuwa ga hanyar Allah. 

Sannan har wa yau ya kamata mu yi la’akari da koyarwar addini da ta ce a yi wa’azi ko faɗakarwa cikin hikima da salo na jan hankali, yadda za a iya shawo kan jama’a ko wanda ake yi wa magana ba tare da an fusata shi ko hassala wasu da ke sauraron karantarwar da ake yi ba. Ko da kuwa iyalinka ne a cikin gida. Kuma a rage amfani da wuraren addini a matsayin cibiyoyin ƙalubalantar gwamnati ko cimma wasu manufofin siyasa.

A nemi wasu hanyoyi da suka dace na isar da saƙonni ga shugabanni da kuma tuntuɓar su game da halin da ƙasa ke ciki ko neman sanin ƙoƙarin da ake yi a ɓangarorin shugabanci daban-daban, domin wayar da kan ’yan ƙasa da yi musu nasiha kan cika alqawuran da za su inganta rayuwar jama’a.

Akwai dabaru da salo iri-iri na wa’azi da za a iya amfani da su, wajen isar da saƙonni na gyara halinka ga shugabanni da sauran ’yan Nijeriya ba tare da zafafawa ko tunzura masu sauraro da sauran mabiya ba.

Kuma kamar yadda na sha faɗa a wannan shafi ƙalubale ne kan hukumomi su samar da wata majalisa ta malamai da masu wa’azi da za su riƙa zama suna tattaunawa kan matsalolin ƙasa da haƙƙoƙinsu na addini da na faɗin albarkacin baki, da kuma sanin haƙƙoƙin da ke kansu a matsayin su na ’yan Nijeriya. Kuma a samar da wani tsari da zai riƙa sa ido yana kula da walwalar malamai da ingancin karatun su, lafiyar ƙwaƙwalwar su da ƙwarewarsu wajen karantarwa. Domin tsaftace harkar ilimantarwa da wa’azi a ƙasar nan.

Bai dace a cigaba da zama sakaka, babu wasu ƙa’idoji ko dokokin gudanar da harkokin addini ba. Hakan shi zai sa a yi maganin baragurbin, cire yaɗa son zuciya da bazuwar gurvatattun aƙidu masu cutar da zaman lafiyar al’umma, da kare martabar koyarwar addini.

Allah shi ne mafi sanin daidai.