An ƙaddamar da tagwayen hanyar da Ƙasar Sin ta gina a Kudu maso Yammacin Kamaru

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, aka ƙaddamar da wata babbar hanyar mota da ƙasar Sin ta gina a kudu maso yammacin Kamaru.

Da yake jawabi a yayin bikin ƙaddamar da aikin, ministan ayyukan jama’a na ƙasar Kamaru, Emmanuel Nganou Djoumessi ya bayyana cewa, buɗe hanyar ya kawo ƙarshen kammala matakin farko na babbar hanyar Kribi zuwa Lolabe.

Yana mai cewa, babbar hanyar za ta sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa da ta mutane daga kowane sashe na ƙasar zuwa tashar ruwan Kribi mai zurfi.

A nasa jawabin ministan kuɗi na ƙasar Louis Paul Motaze, ya bayyana cewa, hanyar wadda kamfanin aikin injiniya na ƙasar Sin mai suna China Harbour Engineering Company (CHEC) ya gina, ta samo asali ne daga haɗin gwiwar kut da kut da ke tsakanin ƙasashen Sin da Kamaru.

Mataimakin babban manajan kamfanin CHEC reshen yankin Afirka ta Tsakiya Zhang Wenfeng,ya bayyana cewa, babban layin da ke kan hanyar Kribi zuwa Lolabe, yana da tsawon kilomita 38.5, kana yana da hanyoyi guda shida, inda aka kebe biyu da ke tsakiya don amfani a nan gaba.

Zhang ya ƙara da cewa, fara aiki da babbar hanyar, zai inganta yanayin kasuwanci a ƙasar Kamaru, da ƙara samar da ayyukan yi, da hanyar tattalin arziki mai haske a faɗin ƙasar.

Fassarawar Ibrahim