An buɗe taron majalisar NPC na bana

Daga CRI HAUSA

Da safiyar yau Asabar ne aka buɗe taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jamaar ƙasar Sin ko NPC a taƙaice, a nan birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar.

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da sauran jagororin ƙasar sun halarci bikin buɗe taron na 5, na majalissar ta 13, a babban ɗakin taruwar jama’a.

Yayin buɗe taron, firaministan Sin Li Keqiang, ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati, a madadin majalisar gudanarwar ƙasar. Cikin rahoton, an sanya burin daga yawan GDPn ƙasar da kaso 5.5 bisa ɗari a shekarar 2022. Kaza lika a shekarar nan ta 2022, Sin na fatan samar da ƙarin sabbin guraben ayyukan yi sama da miliyan 11 a birane, tare da rage adadin marasa ayyukan yi a biranen zuwa ƙasa da kaso 5.5.

Har ila yau, rahoton ya ce, manufar raya tattalin arzikin Sin ba ta sauya ba, inda ake fatan wanzar da ci gaba na tsawon lokaci. Yayin da ƙasar za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau na ɗorewar ci gaba, ciki har da damammakin ƙirƙirar sanao’i, da ingiza ƙirƙire-ƙirƙire, kuma tuni ƙasar ta samu gogewa a fannonin tunkarar ƙalubale da haɗurra.

Rahoton ya ƙara da cewa, ko shakka babu, tattalin arzikin ƙasar Sin zai jure duk wani matsi, zai kuma ci gaba da bunƙasa sannu a hankali tsawon lokaci a tarihi.

Rahoton ya bayyana cewa, ƙasar Sin za ta amfana sosai da jarin ƙasashen waje. Kuma za ta duba yuwuwar nazarin ɓangarorin da ƙasashen waje ba za su iya zuba jari ba, domin tabbatar da an ba su damarmaki kamar takwarorinsu na cikin gida.

A cewar rahoton, ƙasar Sin za ta inganta haɗin gwiwa ƙarƙashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Ɗaya”, da ƙara jajajircewa kan ƙa’idar samun ci gaba na bai ɗaya ta hanyar tuntuba da haɗin gwiwa.

Baya ga haka, ƙasar za ta zurfafa gyare-gyare domin sauƙaƙa hanyoyin biyan harajin kwastam da gina wani tsarin jigilar kayayyaki na ƙasa da ƙasa, domin rage kuɗin da ake kashewa da ƙara inganta cinikayya da ƙasashen ƙetare.

Rahoton ya ƙara da cewa, yarjejeniyar tattalin arziki ta RCEP, ta samar da wani yankin ciniki mara shinge mafi girma a duniya. Kuma ƙasar Sin za ta ƙarfafa gwiwar kamfanoni su yi amfani da fifikon haraji da na asalin kayayyaki, da sauran ƙa’idojin dake ƙarƙashin yarjejeniyar, domin faɗaɗa haɗin gwiwa kan cinikayya da zuba jari.

Har ila yau, ƙasar Sin za ta tattauna tare da cimma yarjejeniyar ciniki cikin yanci mai inganci da ƙarin ƙasashe da yankuna.

Bugu da ƙari, rahoton ya ruwaito cewa, a shirye Sin take ta haɗa hannu da sauran ƙasashe wajen inganta haɗin gwiwa da cimma sakamako na moriyar juna ga kowa.

Faiza Mustapha da Saminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *