Attajirin da ke neman wuce Ɗangote a Afrika ya tafka mummunar asara

Daga AMINA YUSUF ALI

Biloniya, Johann Rupert wanda ya yi ƙaurin suna wajen takara da ganin ya wuce Alhaji Aliko Ɗangote kuma ya maye gurbinsa a matsayin mutum mafi arziki a Afirka ya tafka asarar Dalar Amurka kusan ɗaya da rabi a cikin ƙasa da mako guda. 

Jaridar Ingilishi ta Bloomberg ta rawaito cewa, Johann Rupert ɗin wanda asalinsa xan Afirka ta kudu ne, kuma wanda ya jima yana hararar kujerar Ɗangote ta mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya. Ya tafka asarar, Dala biliyan ɗaya da kusan rabi a cikin kwana biyar kacal.  

Rahotanni sun bayyana cewa, tun daga ranar da aka fara rikici tsakanin Rasha da Yukiren masu zuba hannayen jari a kamfanin nasa suka ja baya, abinda ya jawo masa tafka mummunar asara ta kaso goma sha biyar na dukiyarsa. 

Domin magana ta gaskiya, ‘yan kasuwa daga dukkan sassan Duniya sun tsorata da cewa, kutsen Rasha a Yukiren zai shafi kasuwancin ‘yan kasuwar Rasha.  Musamman ta wajen safarar kayan more rayuwa. Domin kaso 35 na jiragen dakon kaya da safarar su mallakin attajiran ƙasar Rasha ne. Jirgin ruwan dakon kayan da ya fi kowanne tsada ma mallakin babban attajirin nan ɗan asalin ƙasar Rashar nan ne mai suna,  Roman Abramovich.

Amma fa duk da wannan faɗuwar da ya samu a ɓangaren tattalin arziki, har yau Johann Rupert shi ne mutum ma fi arziki a ƙasar da yake, Afirka ta kudu. Kuma har yau shi ne mutum na biyu mafi arziki a Afirka. Wato shi ne yake bin bayan Ɗangote. Har yanzu kamfaninsa na Richemont yana da ƙarfin arzikin da ya kai Dalar Amurka biliyan bakwai. 

Amma dai duk da haka, biliniyoyi na ƙasar Rasha sun samu karayar arziki sosai sakamakon kutsen da ƙasar take yi wa Yukiren a halin yanzu.