23
Apr
Assalam alaikum. Kamar yadda muka sani, mutane na ta yaɗa jita-jitar cewa wai CBN na shirin dakatar da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta internet; Opay da Palmpay, amma Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi ƙarin haske kan waɗannan jita-jita. Babban Bankin ya musanta waɗannan rahotannin inda ya bayyana su a matsayin ƙarya ce tsagwaronta. A cewar rahoto, Daraktan wucin gadi na fannin watsa labarai na Babban Bankin, Mista Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyana hakan 2023, a birnin tarayya Abuja, inda ya ce labarin ƙanzon kurege ne kawai. Rahotannin da aka yi ta yaɗawa waɗanda aka ce sun fito daga bakin…
