Editor

9513 Posts
An mayar wa Juventus maki 15 ɗin da aka kwashe mata a Serie A

An mayar wa Juventus maki 15 ɗin da aka kwashe mata a Serie A

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An mayar da maki 15 da aka kwashe wa Juventus a Serie A, bayan da wata Kotun Sauraren Ƙararrakin wasanni ta yi umarnin a sake bibiyar laifin da ake zargin ƙungiyar. A watan Janairun 2023 aka hukunta Juventus, bayan da aka sami ƙungiyar da laifin bayar da bayanan karya na hada-hadar ƙungiyar. Da wannan hukuncin Juventus ta koma ta uku a teburin Serie A, amma za a iya sake hukuntata idan an sameta da laifin bayan bibiyar zargin da ake mata. Daraktan Tottenham, Fabio Paratici bai yi nasara kan ɗaukaka ƙarar da ya shigar ba, wanda…
Read More
Ɗan Majalisar Wakilai mai jiran gado, Isma’ila Maihanchi ya riga mu gidan gaskiya

Ɗan Majalisar Wakilai mai jiran gado, Isma’ila Maihanchi ya riga mu gidan gaskiya

Zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai na shiyyar Jalingo/Yorro/Zing a Jihar Taraba, Isma’ila Maihanchi, ya riga mu gidan gaskiya. Marigayin ya rasu ne da safiyar Asabar a Abuja bayan fama da rashin lafiya. Kakakin Jam'iyyar PDP, Andeta’rang Irammae, shi ne ya sanar da rasuwar. Ya ce, “Jim kaɗa bayan kammala zaɓen marigayin ya fara rashin lafiya wanda ya ci gaba da karɓar magani a Abuja" inda Allah Ya yi masa cikawa ranar Asabar.
Read More
Osinbajo ya nemi maye gurbin shaidar zama ɗan jiha da ta haihuwa

Osinbajo ya nemi maye gurbin shaidar zama ɗan jiha da ta haihuwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira da a samar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin masu faɗa aji, inda ya buƙaci a aiwatar da tsarin da zai inganta haɗin kan al’umma da haɗin kai a Nijeriya. Osinbajo ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen taron ba da lacca mai taken ‘Policy Making and Good Governance Lecture Series’ wanda Cibiyar Nazarin Dabaru ta Ƙasa (NIPPS) ta shirya. Yayin da ya ke magana kan batutuwan da suka shafi ƙaura, mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira da a maye…
Read More
Har yanzu ban dawo hayyacina ba kan abinda Hakimi ya min – Hiba

Har yanzu ban dawo hayyacina ba kan abinda Hakimi ya min – Hiba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Matar Achraf Hakimi, ɗan ƙwallon ƙungiyar PSG kuma ɗan asalin ƙasar Moroko, wato Hiba Abouk, ta ce, abinda Hakimi ya mata ta kadu sosai, wanda hakan ya sa har yanzu ba ta dawo hayyacinta ba. A shekarar 2020 ne dai suka yi aure da Hakimi inda a yanzu suna da yara biyu, amma sun rabu, matar ta nemi Hakimi ya ba ta rabin dukiyarsa, amma sai lauyanta ya gano Hakimi da sunan mahaifiyarsa ya ke ajiye kadarorinsa. A zantawar da ta yi da kafar Elle, Hiba ta bayyana cewa rabuwarsu ba abu ne me sauƙi ba…
Read More
Indiya ta zarta Chana da yawan jama’a

Indiya ta zarta Chana da yawan jama’a

Indiya za ta wuce Chana a matsayin qasa mafi yawan jama'a a duniya a ƙarshen watan Yuni, alqalumman Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa, hakan zai haifar da babban qalubale ga ƙasar da ke ƙoƙarin samar da ababen more rayuwa daidai lokaccin da ta ke fama da rashin isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasa. Alqaluman sun nuna cewa, yawan al'ummar Indiya ya kai sama da biliyan 1.400 inda ya haura adadin yawan al’ummar Ƙasar Chana da miliyan uku, wanda ke da adadin sama da mutum biliyan ɗaya, inji rahoton hukumar kula da yawan jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya. A baya…
Read More
Abba Gida-gida ya yi miƙa saƙon goron sallah ga Kanawa

Abba Gida-gida ya yi miƙa saƙon goron sallah ga Kanawa

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya miƙa daƙon taya al'ummar Jihar Kano murnar kammala azumin watan Ramadan na bana. A cikin saƙo nasa, Abba Kabir ya buƙaci al'umma a cigaba da ɗabbaƙa kayawawan darussan da aka koya yayin watan azumin da ya ƙare. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar juma'a. Sanarwar ta ce: "Ina tabbatar wa Jama'ar Jihar Kano cewa gwamnati mai jiran gado ƙarƙashin jagorancina za ta samar da hanyoyin da za su…
Read More
Goron Sallah: Babban Hafsan Tsaro ya yi wa Musulmi barka da shan ruwa

Goron Sallah: Babban Hafsan Tsaro ya yi wa Musulmi barka da shan ruwa

Daga BASHIR ISAH Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Lucky Irabor CFR, ya miƙa saƙon taya murnar Ƙaramar Sallah ga ɗaukacin al'ummar musulmin Nijeriya. Janar Irabor ya yi wa Musulmi barka da kammala azumin Ramadana, ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci. Saƙon taya murnar na ƙunshe ne cikin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Tukur Gusau, ya sanya wa hannu, mai kuma ɗauke da kwanan wata 20 ga Afrilu, 2023. Jami'in ya yi addu'ar Allah ya karɓi dukkan ibadun da Musulmi suka gabatar a watan na Ramadan, tare da yi wa Nijeriya fatan nasara. Ya yi amfani…
Read More
Korarren kwamishinanmu na Jihar Adamawa ya yi ɓatan dabo – INEC

Korarren kwamishinanmu na Jihar Adamawa ya yi ɓatan dabo – INEC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ce ba ta da masaniyar inda korarren Kwamishinanta na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya shige tun bayan abin da ya aikata yayin zaɓen cike giɓi na zaɓen gwamnan jihar. Ari ya yi riga malam masallaci wajen sanar da sakamakon zaɓen cike giɓin da aka gudanar tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓen. A cewar INEC, “Ba mu san inda yake ba, saboda tun bayan abin da ya faru Hukumar ta aike masa da wasiƙa ta kuma kira shi a waya. Bai amsa kira ba, kuma shi bai kira ba. “Mun buƙaci ya…
Read More
Bikin Sallah: Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya taya Musulmi murnar Sallah

Bikin Sallah: Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya taya Musulmi murnar Sallah

*Ya buƙaci a dage da addu'a Daga WAKILINMU Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara, Mai Girma Dauda Lawal, ya aike da saƙon taya murna ga ɗaukacin al’ummar Musulmi na Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya bisa ganin ƙarshen watan azumin shekarar 1444 da kuma bikin sallah. A wata takardar sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar wadda Sulaiman Bala Idris ya sa wa hannu, Lawal ya buƙaci al’ummar Jihar Zamfara su zage damtse wurin yin addu’o’i don wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar. Ya ƙara da cewa, watan Ramadana zaɓaɓɓen wata ne daga Allah (SWT) a matsayin watan yin azumi da…
Read More
Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Nijeriya

Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) ta ce akwai akalla fursunoni 3,298 da aka yanke wa hukuncin kisa kuma suke zaman jiran a zartar musu da shi a gidajen kurkukun ƙasar. Kakakin hukumar na ƙasa, Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ranar Laraba a Abuja. Ya ce galibi a Nijeriya ba a cika zartar da hukuncin ba ga waɗanda aka yanke musu ba.Ya ce, “Akwai lokutan rashin tabbas yayin da waɗanda aka yanke wa hukuncin suke ɗaukaka kara zuwa kotuna na gaba. “Fursunonin da…
Read More