24
Apr
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya amince da maida wa Sarkin Birnin Yandoto, Aliyu Marafa, rawaninsa bayan dakatar da shi da aka yi. Idan ba a manta ba, a baya an dakatar da Marafa ne sakamakon naɗa ɗan ta'dda, Ado Aliero, da ya yi a matsayin Sarkin Fulani a watan Yulin 2022. Wanda a sakamakon hakan gwamnatin jihar ta kafa kwamitin na musamman domin gudanar da bincike kan abin da Sarkin ya aikata. Sai dai, sanarwar da Sakataren Gwamnatin Zamfara, Kabir Balarabe, ya fitar, ta ce an maida Marafa kan muƙaminsa bayan sakamakon binciken kwamitin ya nuna Sarkin ba shi…
