Editor

9513 Posts
Jami’ar Bayero ta yi rashi

Jami’ar Bayero ta yi rashi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Hukumar Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da rasuwar magatakardarta, Malam Jamil Ahmad Salim, a safiyar ranar Laraba. Tun da farko an wallafa sanarwar ne a shafin Facebook na Jami’ar ta BUK, inda ake sanar da al’ummar Musulmi guri da lokacin da za a yi jana’izar marigayin. Sanarwar ta ƙara da cewa, za a yi jana’izar marigayin da misalin ƙarfe goma na safe a Babban Masallacin Juma’a da ke sabuwar jami’ar da ke kan titin zuwa Gwarzo a birnin Kano.
Read More
Buhari: Ga wani darasi

Buhari: Ga wani darasi

Daga SHAFI’U DAUDA GIWA Wannan bawan Allah shi ne wanda ya fi kowa farin jini a tarihin ƙasarmu Nijeriya. Ɗaruruwan mutane sun rasa ransu saboda murnar zaɓen da ya ci a shekarar 2015. An yi lokacin da ko takarar kansila mutum ya tsaya sai ya haɗa hotonsa da na Buhari don ya ɗosani farin jini. ‘Yan siyasa bila’adadin sun ci zaɓe a sanadiyyar ɗaga hannunsu da Buhari ya yi, tun kafin ya ci nasa zaɓen a shekarun baya tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011 Allah kaɗai ya san adadin mutanen da shugaba Buhari ya ɗaga wa hannu suka kai labari Waɗansu…
Read More
Goman Ƙarshe: Da gaske mata addu’ar neman miji suke yi a tahajjud? (II)

Goman Ƙarshe: Da gaske mata addu’ar neman miji suke yi a tahajjud? (II)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A yau za mu cigaba daga inda muka tsaya a makon ga ya gabata. Kamar misalin yadda Farfesa Fatima ta bayar ne, inda take cewa wasu iyaye masu kwaɗayin abin duniya suna taimakawa wajen daɗewar ’ya’yansu mata a gida, domin kuwa sun mayar da su tamkar wata hajar neman kuɗi, suna jiran sai wani babban mutum ko ɗan masu kudi ne zai fito su aura masa, saboda tunanin auren zai zama musu tsani na kai wa ga buƙatun su na rayuwa. Haka zalika su ma samarin yanzu idon su ya rufe da neman kuɗi domin su…
Read More
Zuwa ga ‘yan mata da zawarawa: Hattara da samarin shaho!

Zuwa ga ‘yan mata da zawarawa: Hattara da samarin shaho!

Daga AMINA YUSUFU ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinku na zamantakewa a jaridarmu mai farin jini ta Manhaja. Kamar yadda kuka gani a take, kira ne ga 'yammata da zawarawa a kan su guje wa wasu nau'in samari da ake kira da samarin shaho. Na san mai karatu zai shiga kogin tunani a kan su waye samarin shaho kuma? Samarin shaho ba wasu ne ba face samarin da za su zo wajen budurwa ba da niyyar aurenta ba sai don su rage lokaci, ko kuma don su ɓata mata rayuwa su gudu. Abinda ya…
Read More
Kano ce ta uku a jihohin da aka fi kiran wayar salula da Internet– NBS

Kano ce ta uku a jihohin da aka fi kiran wayar salula da Internet– NBS

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, wato NBS, ta bayyana Jihar Kano a matsayin ta uku a jerin jihohin da suka fi amfani da wayar salula da Internet a ƙasar. Sauran jihohin su ne Legas a matsayi ta ɗaya, sai Ogun a matsayin ta biyu. A wani rahoto da ta saba fitarwa duk bayan watanni uku, NBS ta yi bayani kan harkokin tarho, wanda ya ƙunshi bayanai na watannin ukun ƙarshe na shekarar 2022. Bayanan sun haɗa da na adadin masu kiran waya, da masu amfani da intanet, da kuma yawan masu amfani da kowane kamfanin sadarwar…
Read More
Alfanun tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen duniya

Alfanun tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A baya mun duba tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen, da dalilan da suka kai su in ma ta hanyar fatauci ne, ko cinkayyar bayi. Baya ga haka mun ga ire-iren ƙasashen da suka je kamar Tiripoli da ke Libiya da Chadi, da Turai kamar kudancin Amurka da suka haɗa da Brazil da sauransu. A bisa kyakkyawan bincike da nazari, duk inda aka samu wata al’umma tana gudanar da harkokin rayuwarta to, nan ne take tafiyar da al’amuran rayuwarta da suka haɗa da al’adunta da amfani da harshenta wanda shi ne harshen adabi mai nuna irin azancinta…
Read More
Yadda ɗan ƙwallo, Achraf ya sha matarsa tauraruwar fim, Hiba da basilla

Yadda ɗan ƙwallo, Achraf ya sha matarsa tauraruwar fim, Hiba da basilla

Daga AISHA ASAS  A 'yan kwanakin nan ne dai kafafen sada zumunta suka yi sabon ango, wanda ya kasance abin sha'awar kowacce uwa, mafi wayo a wurin kowanne magidanci, kuma abin haushin mafi yawa daga cikin mata. Achraf Hakimi, ɗan wasan tamaula da ya kafa tarihin da ba a taɓa samun sa ba a tsakanin mutane masu suna da shuhura. Kamar yadda yake sananne a tsakanin ƙasashe da dama idan ka cire Nijeriya, saki wani abu ne mai matuƙar wahalar yi, tare da hasara musamman ma ga miji, domin doka ce, mace na da dama kan wani kaso na dukiyar…
Read More
Manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na sa’o’i 72

Manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na sa’o’i 72

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antony Blinken, ya bayyana cewa, manyan sojojin Sudan sun amince da tsagaita wuta na kwana uku daga ranar Talata. Blinken ya ce, “Biyo bayan tattauna mai zafi na sa'o'i 48, Rundunar Sojojin Sudan (SAF) da Rundunar RSF sun amince da matakin tsagaita wuta a faɗin ƙasar na sa'o'i 72 hours." Ya karatda cewa, “Amurka ta yi kira ga SAF da RSF da su tabbatar da tsagaita wutar nan take kamar yadda aka cimma." Haka nan, ya ce Amurka na aiki tare da abokan hulɗa don kafa kwamitin da zai tattauna batun tabbatar da tsagaita wuta na…
Read More
Yau Shugaba Buhari zai tafi Ghana

Yau Shugaba Buhari zai tafi Ghana

A wannan Talatar ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai ziyarci ƙasar Ghana don halartar taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra, babban birnin ƙasar. Hakan na ƙunshe ne ciki wata sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta wallafa a shafinta na Tiwita a ranar Litinin. Sanarwar ta ce, ta ce shugaban zai bar Nijeriya ranar Talata, 25 ga Afrilu domin halartar taron, wanda Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Akuffo-Ado, zai jagoranta. Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu…
Read More
‘Yan bindiga sun sace jami’ar Shirin Ƙidaya, sun nemi a biya fansar N500m

‘Yan bindiga sun sace jami’ar Shirin Ƙidaya, sun nemi a biya fansar N500m

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinar Tarayya mai wakiltar Jihar Bayelsa a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, Mrs Gloria Izonfuo. Majiyarmu ta ce an sace Gloria ne da yammacin Lahadi a yankin mararrabar Ogbakiri cikin Ƙaramar Hukumar Emohua a Jihar Ribas. Bayanai sun ce Kwamishinar na kan hanyarta ta zuwa Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas, bayan ta baro Ƙaramar Hukumar Brass da ke Jihar Bayelsa. An ce 'yan bindigar sun tsare motarta ne a kan babbar hanyar yanki inda suka yi awon gaba da ita tare da direbanta. Haka nan, an rawaito cewar 'yan bindigar sun buƙaci a biya su…
Read More