21
Nov
Daga BASHIR ISAH A wani samame da Rundunar Mayaƙan Sama ta Nijeriya (NAF) ta kai da jirigin yaƙinta a Jihar Zamfara, Rundunar ta samu nasarar kashe Malam Ila wanda ya yi ƙaurin suna waje safarar makamai a ƙauyen Manawa cikin Ƙaramar Hukumar Shinkafi a jihar. Majiyar PRNigeria ta ce, Ila shi ne babban mai yi wa ‘yan ta’adda safarar makamai, musamman ma Bello Turji a Zamfara. Majiyar ta ce, “A ranar 18 ga Nuwamban 2022 NAF a ƙarƙashin Operation Hadarin Daji suka kai samamen inda aka hallaka Malam Ila. “Malam Ila ya kasance wanda ake nema ruwa a jallo saboda…
