Editor

9513 Posts
Naira ta faɗo warwas zuwa 730 a Dala ɗaya

Naira ta faɗo warwas zuwa 730 a Dala ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Nairar Nijeriyar dai ta faɗo zuwa wani sabon matsayi, inda a safiyar Alhamis ɗin nan an sayar da Naira 730 a kasuwar ƙasa, wanda ya ragu da kashi 0.69 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata. Faɗuwar darajar canjin ta biyo bayan matakin da babban bankin ƙasar ya ɗauka na ɗaga darajar kuɗin ruwa zuwa sama da shekaru 20 sama da kashi 15.5 cikin ɗari, wanda ke nuna ƙaruwar kaso 150 daga kashi 14% da aka bayyana a taron MPC da ya gabata. Farashin da ya kai Naira 730 a dala shi ne mafi girma…
Read More
Ƙasar Sin za ta ɗauki sabbin ‘yan sama jannati da za su dudanar da binciken sararin samaniya a nan gaba

Ƙasar Sin za ta ɗauki sabbin ‘yan sama jannati da za su dudanar da binciken sararin samaniya a nan gaba

Daga CMG HAUSA Hukumar kula da binciken sararin samaniyar ƙasar Sin (CMSA), ta sanar a jiya Lahadi cewa, ƙasar za ta ɗauki sabbin ‘yan sama jannati 12 zuwa 14, waɗanda za su gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya a nan gaba. Daga cikin ‘yan sama jannatin da ke cikin shirin ko-ta-kwana, kana rukuni na huɗu na ‘yan sama jannatin ƙasar, bakwai zuwa takwas daga cikinsu za su kasance matuƙa kumbunan sama jannati, biyar zuwa shida daga cikinsu za su kasance injiniyoyin kumbunan sama jannati da ƙwararru masu kula da gwaje-gwaje, ciki har da guda biyu a matsayin ƙwararru masu kula…
Read More
Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (3)

Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (3)

Daga AISHA ASAS A wannan satin muke son kai ƙarshen wannan darasin na mu da muka shafe sati biyu muna kawo wa masu karatu, kuma idan har kuna biye da mu, mun faro ne da gabatar da ita kanta matsalar ta kogon haƙora, yadda ta ke samuwa zuwa dalilin yawaitar ta, ba mu tsaya ko'ina ba sai a wasu daga cikin hanyoyin da za a iya magance matsalar cikin sauƙi. A wannan satin ma dai za mu kawo wata hanyar ce da ta sha banban da waɗanda muka kawo a baya. Amfani da man kwakwa: Man kwakwa na da ƙarfi…
Read More
Dandalin shawara

Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Aunty Asas ina wuni. Ya aiki. Dan Allah ki taimaka min da shawarar yadda zan yi. Wallahi Ina son in yi aure, sai dai na kasa samun irin mijin da na ke so. Ina son kyakyawan namiji da tun a ganin farko zai kamu da matsananciyar soyayyata. Mu yi soyayya da za ta burge duk wanda ya gan mu. Ya zamana ba wanda zai kula sai ni kaɗai. Irin ko faɗa muka yi har jikinshi ya nuna yana cikin damuwa. Mai kuɗi da yawa, wanda ya iya girki don idan ba ni da lafiya. Wanda ba…
Read More
Masu ruwa da tsaki a Bankin Sterling sun amince da sauya wa bankin suna

Masu ruwa da tsaki a Bankin Sterling sun amince da sauya wa bankin suna

Daga AMINA YUSUF ALI Bankin Sterling zai sauya suna bayan Sahalewar masu ruwa da tsaki. A yanzu haka sunan bankin kaɗai wanda aka sani da bankin ba da rance zai sauya i zuwa shugaban rukunin bankunan hada-hadar kuɗi. Wannan jawabi ya fito ne daga bakin mahukuntan bankin. Inda aka bayyana hakan ranar Litinin ɗin da ta gabata. Inda aka ƙara da cewa, yanzu kawai takardar amincewar masu ruwa da tsakin bankin kawai ake jira don zartar da wancan hukuncin. A cewar su, bankin zai samu iko a kan kamfanonin da yake da hannayen jarinsa a ciki. Wannan sanarwar ta zo…
Read More
Rasuwar Sha’awa: FIDA da ƙungiyoyi 20 za su ɗaukaka ƙara – Barista Bilkisu

Rasuwar Sha’awa: FIDA da ƙungiyoyi 20 za su ɗaukaka ƙara – Barista Bilkisu

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Ƙungiyar Lauyoyi Mata (FIDA), ƙarƙashin jagorancin Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman, da wasu ƙungiyoyin jin ƙai 20 sun sha alwashin bin digdigi da haƙƙi na ganin an tabbatar da adalci ta hanyar shari'a kan duk wanda aka samu da laifin a rasuwar Sha'awa Abdullahi mai juna biyu da ta rasa ranta a Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano. Marigayiyar ta rasu ne sakamakon sakaci da rashin kayan aiki a lokacin da ta ke buƙatar kulawa gaggawa yayin da ta ke naƙudar haiwuwa a asibitin don neman taimakon jami`an lafiyar asibitin, kamar yadda yar uwarta…
Read More
Kar ku katse zumunci a tsakaninku, Maikuɗi Dogo ga al’ummar Tafa

Kar ku katse zumunci a tsakaninku, Maikuɗi Dogo ga al’ummar Tafa

Daga MUHAMMAD ALI a Tafa Shugaban Ƙungiyar Zumunta da Taimakon Jama'a, wadda ake 'Community Development Association' a Turance, da ta ke garin Tafa ta ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, Alhaji Maikuɗi Dogo, ya yi kira ga al'ummar garin, da kada su sare wajen cigaba da zumunci da zamantakewar da aka sansu da shi shekara da shekaru a tsakaninsu. Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke hira da manema labarai yayin gudanar da babban bikinsu na Ajo da suka saba shiryawa akai-akai a harabar ƙungiyar da ke garin na Tafa a ƙarshen mako, inda ya yi…
Read More
2023: An fara kamfen

2023: An fara kamfen

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Doguwar dimokuraɗiyyar Nijeriya ta shiga shekara ta 24 bana daga fara ta a 1999. Bayan dogon mulkin soja an samu nasarar komawa tafarkin dimokuraɗiyya a Nijeriya inda tun a na fargabar za a samu dawowar sojoji har ta kai ga ’yan siyasa yanzu sun warware kafa su na mulkin su bisa tsarin mulki da ya raba turakun gwamnati su ka zama uku wato sasahen zartarwa, majalisa da kuma sashen shari’a. Jamhuriya ta farko ta yi kimanin shekara 6 ne inda sojoji su ka yi juyin mulkin da su ka zubar da jinin farar hula a 1966.…
Read More
Wasu shugabannin Afirka sun taya Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin murnar cika shekaru 73 da kafuwa

Wasu shugabannin Afirka sun taya Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin murnar cika shekaru 73 da kafuwa

Daga CMG HAUSA A baya-bayan nan, shugabannin ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama ne, suka bugu waya ko aiko da wasiƙu ga Xi Jinping, babban sakataren kwamitin ƙolin JKS, kuma shugaban jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, don taya murnar cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, tare da fatan samun nasarar gudanar da babban taron wakilan JKS karo 20 dake tafe. A saƙonsa, shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi fatan babban taron wakilan JKS karo na 20, wanda ke da ma’ana a tarihi, zai gudana cikin nasara. Ya kuma bayyana cewa, yana fatan taron zai fito…
Read More
Ƙasashen duniya sun nuna goyon baya ga shawarar samun bunkasuwar duniya

Ƙasashen duniya sun nuna goyon baya ga shawarar samun bunkasuwar duniya

Daga CMG HAUSA A watan Satumba na shekarar 2021, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarar samun bunƙasuwar duniya bisa taken “yadda za a samu bunƙasuwar duniya da salon bunƙasuwar da ake fatan samu a duniya”. A cikin sama da shekara ɗaya, ƙasa da ƙasa sun nuna goyon baya ga wannan shawara. Ya zuwa yanzu, ƙasashe fiye da 100 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama ciki har da MƊD, sun nuna goyon baya ga shawarar, kana ƙasashe fiye da 60 sun shiga rukunin haɗin gwiwa na raya shawarar samun bunƙasuwar duniya. Babban sakataren MƊD António Guterres ya…
Read More