24
Mar
Daga BASHIR ISAH Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana adadin ɗaliban Kuriga da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga. An yi garkuwa da ɗaliban ne a makarantar firamare da sakandare na yankin Kuriga da ke cikin Ƙaramar Hakumar Chikun a Jiahar Kaduna. Cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun Manjo-Janar Edward Buba, rundunar ta ce ɗalibai kimanin 137 ne aka yi nasarar cetowa, saɓabin abin da wasu rahotanni suka rawaito. Kimanin ɗalibai 287 ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da su ranar 6 ga Maris a yankin Kuriga, lamarin da ya tada hankalin jama’a a ciki da wajen Nijeriya. Sanarwar…
