23
Mar
Daga BASHIR ISAH A ƙalla 'yan bindiga, ɓarayin daji da tsageru 97 ne Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya bayyana a matsayin waɗanda yake nema ruwa a jallo. Ofishin ya ce waɗanda yake neman suna da hannu wajen aikata manyan laifuka da tada zaune tsaye a sassan ƙasa. Har wa yau, waɗanda lamarin ya shafa ya haɗa da shugaban wani ɓangare na tsagerun IPOB, wato Simon Ekpa. Mai magana da yawun rundunar soji, Manjo-Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana sunaye da hotun waɗanda rundunar ke farautarsu. MANHAJA ta rawaito a makon jiya cewa, Babban Ofishin tsaro na shirin…
