22
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Bursari a Jihar Yobe, Hon. Lawan Bukar ya bayyana cewa ba su da abinda za su ce wa gwamnan jihar Mai Mala Buni sai sam-barka, domin a cewarsa yana iyakacin ƙoƙarinsa na ganin ya sauke nauyin da al'ummar jihar ta ɗora masa. Bukar ya ce Gwamna Buni ya tallafa wa kananan hukumomin jihar wajen ƙarfafa wa da inganta rayuwar jama'a musamman masu ƙaramin ƙarfi da gidajen marayu; samar da aikin yi ga matasa a ƙaramar hukumar Bursari da suka haɗa da: Samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a cikin…
