Editor

9513 Posts
Majalisar Dattawa ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rance ta 2024

Majalisar Dattawa ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rance ta 2024

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rancen karatu ta 2024 wanda ɗalibai a manyan makarantu za su ci gajiya. Majalisar ta amince da hakan ne bayan da ta karɓi rahoton Kwamitin Majalisar kan Manyan Makarantu da asusunTETFUND. Shugaban Kwamitin, Sanata Muntari Dandutse (APC – Katsina ta Kudu), shi ne ya gabatar da rahoton yayin zaman malajisar a ranar Laraba. Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dattawa da ta wakilai buƙatar neman soke dokar bai wa ɗalibai rancen karatu (ga…
Read More
Zargin $300m: Majalisar Wakilai ta yi barazanar tsare ministan lafiya muddin ya ƙi amsa gayyatarta

Zargin $300m: Majalisar Wakilai ta yi barazanar tsare ministan lafiya muddin ya ƙi amsa gayyatarta

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Majalisar Wakila kan yaƙi da zazzaɓin Maleriya, HIV/AIDS da Tarin Fuka, ya bai wa Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, sa’o’i 72 kan ya bayyana a gabanta ko kuma ta sa a kamo shi. Gayyatar ta shafi har da Babban Sakatariyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, wato Daju Kachollom. Majalisar ta buƙaci Pate da Kachollom su abayyana a gabanta ne domin amsa tambayoyi kan zargin karkatar da Dala miliyan 300 da aka ware domin yaƙi da zazzaɓin maleriya tun daga 2021. Kwamitin ya yanke shawara kan cewar a damƙo Babbar Sakatariyar muddin ta ƙi amsa gayyata, saboda…
Read More
Sojoji sun ceto mutum 16 a hannun ‘yan bindiga a Katsina

Sojoji sun ceto mutum 16 a hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jami'an soji dake da sansani a Marabar Mai-Gora sun samu nasarar ceto waɗansu mutane da 'yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su tun kimanin kwanaki 46 da suka wuce. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da mata 10 da kuma ƙananan yara shida. Sojoji sun taki wannan nasarar ce a lokacin da suke gudanar da sintiri a garin Rimi. Wadanda aka ceto ɗin, na daga cikin mata 54 da barayin daji suka sace a hanyar Gamji zuwa Ɗandume a farkon watan Fabarairun da ya gabata. Sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina,…
Read More
Farfesa Suleiman na NSUK ya taka rawar gani – Dokta Suleiman

Farfesa Suleiman na NSUK ya taka rawar gani – Dokta Suleiman

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Shugaban Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya na Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Dokta Abdullahi Suleiman Mohammed, ya ce babu shakka takwaransa na Jami'ar Jihar (NSUK), wato f'Farfesa Suleiman Bala Mohammed, ya taka rawar gani wajen haɗa kawunan shugabannin manyan makarantun da ke faɗin Jihar. Dokta Suleiman ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattauna da wakilin mu a ofishin sa dake kwalejin ranar Laraba ta wannan makon Ya ce Farfesa Suleiman wanda wa'adin mulkin sa zai ƙare a watan Maris da ake ciki, kafin yanzu ya yi ƙoƙarin haɗa kawunan takwarorinsa don ci…
Read More
Gobara ta laƙume gidaje a Legas

Gobara ta laƙume gidaje a Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da aukuwar gobara a wasu jerin gine-gine guda uku kusa da ke Dosumu- Idomota, a yankin Lagos Island a Jihar Legas. Majiyarmu ta ce gine-ginen da lamarin ya shafa, benaye ne masu hawa uku da huɗu. Ya zuwa haɗa wannan labari, NEMA ta ce ba a kai ga gano dalilin tashin gobarar ba. Jami’in NEMA, Ibrahim Farinloye, ya ce hukumar ta fuskantar ƙalubale wajen ƙoƙarin kashe gobarar.  “Muna fuskantar babban ƙalubale wajen samun ruwan da za a yi amfani da shi wajen kashe gobarar,” in ji shi. Ya…
Read More
Kin iya kunu? (2)

Kin iya kunu? (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku mai albarka na zamantakewa mai zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Da farko ina taya ku murnar shigowar watan azumi na Ramadan watan rahama watan yafiyar zunubai. Dafatan za mu dage da zikiri da ambaton Allah da istigifari don rabauta da wannan gwaggwavan lada. A makon da ya gabata mun fara bayani a kan sirrin madafi. Wato a game da tambayar mata sun iya kunu? Ba kunun kaɗai ba, kin san sirrin tukunya? A makon da ya…
Read More
Iyaye ku ja ‘ya’yanku masu nakasa a jiki don kwanciyar hankalinsu – Fatima Bello

Iyaye ku ja ‘ya’yanku masu nakasa a jiki don kwanciyar hankalinsu – Fatima Bello

"A dena ɗora wa aljannu alhakin matsalar nakasa" Daga ABUBAKAR M. TAHEER Fatima Bello matashiya ce da ta ke taimakon yara masu buƙatar ta musamman, inda ta buɗe gidauniyar tallafa musu mai suna Haske Children Foundation. A cikin wannan tattaunawa da wakilin Manhaja, Abubakar M Taheer ya yi da ita, ta nuna takaicin ta kan yadda al'umma suka ɗauki masu buƙata ta musamman a matsayin wani abu da ya shafi aljannu, dama wasu batutuwa da ya shafi taimakon masu buƙata ta musamman. A sha karatu lafiya. MANHAJA: DA farko za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu.…
Read More
Na’ibin limamin masallacin gidan Sarkin Kano, Malam Nazifi ya rasu

Na’ibin limamin masallacin gidan Sarkin Kano, Malam Nazifi ya rasu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Allah ya yi wa na’ibin limamin masallacin Juma’a na gidan sarki, Malam Nazifi Muhammad Ɗalhatu, rasuwa a yammacin Talata. Rahotanni sun bayyana cewar Marigayin ya rasu yana da shekaru 81, bayan fama da rashin lafiya. An yi jana’izarsa a harabar masallacin gidan Sarkin Kano da ke Ƙofar Kwaru. Rahotanni sun ce jama'a da dama ne suka halarci jana’izar ne, daga ciki har da Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauransu.
Read More
Gwamna Sule ga Peter Obi: Zai fi maka ka riƙa mara wa Tinibu baya

Gwamna Sule ga Peter Obi: Zai fi maka ka riƙa mara wa Tinibu baya

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya shawarci ɗan takaran shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour, Mista Peter Obi, kan ya riƙa bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinibu cikakken goyon baya a ƙoƙarin da yake yi na kai ƙasar nan mataki nagaba. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da Obi ya ziyarce shi a Gidan Gwamnati dake birnin Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, a rabar Litinin, 18 ga Maris, 2024. Gwamna Sule ya gode wa Peter Obi dangane da ziyarar ta musamman da ya kai masa, inda ya ce Obi yana da komai da…
Read More
Lawal ya kama hanyar bunƙasa Asibitin Ƙwararru na Zamfara

Lawal ya kama hanyar bunƙasa Asibitin Ƙwararru na Zamfara

*Ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa Karo na 19 Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya amince da a yi wa Asibitin Ƙwararru na Yeriman Bakura kwaskwarima domin cimma buƙatun kiwo lafiya yadda ya kamata a jihar. Lawal ya amince da wannan aikin ne yayin zaman Majalisar Zartarwar karo na 19 wanda ya jagoranta a ranar Litinin a Fadar Gwamnatin jihar da ke Gusau, babban birnin Jihar. Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ta ce aikin gyaran asibitin zai kan kama ba tare da ɓata lokaci ba, inda ake sa ran bunƙasa cibiyar…
Read More