Editor

9513 Posts
Yadda jarumi Ali Nuhu ya karɓi ragamar aiki a matsayin Shugaban NFC

Yadda jarumi Ali Nuhu ya karɓi ragamar aiki a matsayin Shugaban NFC

Daga AISHA ASAS A ranar Talata da ta gabata ne, shahararren jarumi a masana’antar Kannywood Dakta Ali Nuhu ya kama aiki a hukumance a matsayin Shugaban Hukumar Finafinai ta Qasa (NFC) tare da alƙawarin hanzarta kawo cigaba a masana’antar finafinan Nijeriya. Bayanin wanda ya fito daga wurin Daraktan Ya daa Labarai na hukumar, Mista Brian Etuk. A sanarwar wadda ya gabatar ga ‘yan jarida, Mista Brian ya ce, a ƙwarya-ƙwaryar bikin miqa mulki da aka gudanar a shelkwatar hukumar da ke Jos ta Jihar Filatu, wanda ya samu halartar manyan baqi, da suka haɗa da jiga-jigan masana’antar fim, ma’aikatan hukumar…
Read More
Hukumar tace finafinai ta bada umurnin rufe dukkan gidajen gala da ke Kano

Hukumar tace finafinai ta bada umurnin rufe dukkan gidajen gala da ke Kano

Daga AISHA ASAS Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha ta bayar da umurnin kulle duk wani gidan gala da ke faɗin Jihar Kano. Wannan na daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi na tarbon wata mai tsarki, watan Ramadana. Sanarwar wadda ta fito ta hannun jami’in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman. A cewar sanarwar, hukuncin na zuwa ne bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin koungiyar ta masu gidajen gala a ofishinsa. Kamar yadda ya bayyana, shugaban hukumar Abba El-Mustapha, ya ce, dokar za ta fara aiki ne a ranar…
Read More
Illar cin hanci da cin dunduniya

Illar cin hanci da cin dunduniya

Assalamu alaikum! Yawancinmu ’yan Nijeriya mu kan kasance Jahilan masu ilimi ne, wato za ka ga cewa duk da cewa mun yi mu’amala iri-iri ta rayuwa kuma mun je makaranta mun sami difloma, digiri ko digirgir, tunanin mu yakan kasance a gajeriyar mahanga yadda komai mu ke kallonsa daga ɓangaren yanki, addini ko ƙabila, kamar yadda malamai ke yawan cewa, shi jahilci ba wai kawai yana nufin rashin iya karatu ko rubutu ba ne, fyace ana aiki da shi yadda ya kamata. Mu yi ƙoƙarin ganin ba mu zama misalin Jaki da kaya ba. Mun kasa gane cewa manyan ƙasarnan…
Read More
Sojoji sun ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su a Kajuru

Sojoji sun ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su a Kajuru

Daga BASHIR ISAH Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa, dakarun da aka tura Jihar Kaduna ƙarƙashin shiyyar 1 Division, sun samu nasarar ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Tantatu cikin yankin Ƙaramar Kajuru a jihar. Ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a ranar Talata. Rundunar ta ƙara da cewa, bayan da maharan suka yi garkuwa da wasu mutanen ƙauyen Tantatu a ranar 17 ga Maris, 2024, daga baya dakarun suka bi sawun ɓarayin. "Bayan da suka isa wurin da lamarin ya faru, cikin ƙwarewa dakarun suka bi sawun maharan tare kuma da…
Read More
Jerin sunayen sojoji 15 da suka cimma ajali a Delta

Jerin sunayen sojoji 15 da suka cimma ajali a Delta

Daga BASHIR ISAH Rundunar Sojin Nijeriya ta fiitar da jerin sunayen dakarunta da suka rasa rayukansu a bakin aiki a Jihar Delta kwanan nan. Sojojin da lamarin ya shafa suna aiki ne a bataliya ta 181 Amphibious Battalion, sun mutu ne yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya domin kwantar da tarzoma a ƙaramar hukumar Bomadi ta jihar Delta sakamakon ɓarkewar rikici. Rundunar ta ce sojojinta 15 tsagerun Niget Delta suka yi wa kisan gilla. Jami'an da lamarin ya shafa sun haɗa da: – LT COL AH ALI COMMAND OFFICER 181 AMPHIBIOUS BATTALION NIGERIAN ARMY – Maj SD Shafa…
Read More
Ina mafita ga Almajiranci?

Ina mafita ga Almajiranci?

Assalamu alaikum. A yau zan aika buɗaɗɗiyar wasiƙa ne na ina mafita ga Almajiranci a Nijeriya. Almajiranci na da ma’ana guda biyu, wato tsarin koyar da ilimin addinin musulunci a ƙasashen yammacin Afirka, musamman a arewacin Nijeriya, yadda ake tura yara wajen Malamai a wasu garuruwa domin yin karatun Ƙur’ani. Ɗaya ma’anar ita ce ta tsarin da irin waɗannan ɗalibai da kuma waɗanda ba ɗaliban ba ke yawo su na barar abinci ko kuɗi. Almajirancin da mu ke gani a yanzu ya sha banban da wanda aka gada a can baya. A baya almajiranci shine rumbun da ake samar da…
Read More
An tsinci jariri a Nasarawa

An tsinci jariri a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Wani matashi mai suna Yakubu Sule ya sinci wani jariri mai watanni biyu kacal da haihuwa wanda har yanzu ba a san wace ta jefar da shi a wata unguwa da ake kira Unguwar Maina dake birnin Lafiya, Jihar Nasarawa ba. Binciken wakilin mu ya gano cewa an tsinci jaririn ne shinfiɗe a ƙasa a ƙofar wani gida dake kusa da ofishin hukumar kula da gidan yari a da ke Unguwar Maina ɗin. Da yake bayyana wa wakilin mu yadda lamarin ya auku, wanda ya tsinci jaririn, wato Yakubu Sule ya ce, ya ga…
Read More
Delta: ‘Dole waɗanda suka kashe sosjoji su fuskanci hukunci’ — Tinubu

Delta: ‘Dole waɗanda suka kashe sosjoji su fuskanci hukunci’ — Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tir da kashe sojoji da aka yi a Jihar Delta, yana mai cewa dole waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin su fuskanci hukunci. Kwanan nan ne aka kashe wasu sojoji 15 a jihar ta Delta, ciki har da manjo guda biyu, kyaftin ɗaya, sai kuma ƙananan sojoji 12 da farar hula ɗaya. Lamarin ya faru ne a yankunan Okuama da Ughelli a makon da ya gabata a lokacin da suka tafi aikin kwantar da tarzoma. Sai dai, da yake maida martani kan lamarin a cikin sanarwar da ya fitar da yammacin…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 87 a wani sabon hari a Kaduna

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 87 a wani sabon hari a Kaduna

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Kaduna sun yi garkuwa da mutum 87 a wani sabon harin da suka kai yankin Tashar Kajuru da ke jihar. Wani matashi a yankin mai suna Harisu Dari, shi ne ya tabbatar da aukuwar hakan ga majiyarmu a ranar Litinin. Wannan na zuwa ne bayan wasu 'yan kwanaki da 'yan bindigar suka hari a yankin Dogon Noma da kuma kauyen Kuriga inda suka sace ɗailiban firamare su sama da 200. Bayanai sun ce, maharan sun kuma fasa shaguna inda suka kwashi kayayyaki da dama yayin harin. Yawan hare-haren ta'addancin da ke aukuwa a…
Read More
Gobara ta laƙume wani sashen Babbar Kasuwar Sakkwato

Gobara ta laƙume wani sashen Babbar Kasuwar Sakkwato

Daga BASHIR ISAH Rahotanni da muka samu daga jihar Sakkwato na nuni da cewa, an samu aukuwar gobara a Babbar Kasuwar Sakkwato. Bayanai sun ce gobarar ta fi ƙamari a sashen masu sayar da bababura a kasuwar. Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin aukuwar gobarar, sai dai MANHAJA ta tattaro cewar da safiyar ranar Litinin iftila'in ya auku. Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Babura a Kasuwar, Shehu Muhammad, ya ce ba a kai ga gano adadin ɓarnar da gobarar ta yi ba saboda rashin tsagaitawar wutar. An ga jami'an kashe gobada na jiha da na tarayya a wurin…
Read More