Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga a Bauchi sun kashe basarake sa’o’i 24 bayan sun yi garkuwa da shi

‘Yan bindiga a Bauchi sun kashe basarake sa’o’i 24 bayan sun yi garkuwa da shi

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Bauchi sun kashe Dagacin ƙauyen Riruwai, Alhaji Garba Bafamasi, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Toro a jihar. MANHAJA ta kalato cewar, 'yan ta'addan sun kashe basaraken ne sa'o'i 24 bayan da suka yi garkuwa da shi. Rahotanni sun ce a ranar Juma'a, 15 ga Maris, 'yan bindigar suka dira fadar Alhaji Badamasi inda suka razanar da jama'ar yankin da harbin bindiga kafin daga bisani suka yi awon gaba da shi. Majaiyarmu ta ce, 'yan bindigar ba su damu da kiran 'yan basaraken don neman fansa ba, lamarin da ya sa aka kasa gane…
Read More
Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

Dandalin shawara: Na reni ‘ya’ya uku da mijina ya haifa a waje ba tare da sani na ba

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Barka da safiya malama Aisha. Na san ba ki san ko wacce ce ni ba, sunana…………kuma na samu number ki ta hannun Hajiya…………ƙawata ce, lokacin da na ke mata bayanin halin da nake ciki ne, sai ta ce, ga number na kira ki, ke ce wadda ki ka zo har gida lokacin da matsalarta da……………..ta yi tsanani, ke ki ka taimaka har aka samu mafita. Malama Aisha, mijina ne can baya shekaru da yawa, shi da wani wan babanshi suka shigo da yamma, wan baban nasa ɗauke da jinjiri,…
Read More
Ningi: Nijeriya iya ruwa fidda kai!

Ningi: Nijeriya iya ruwa fidda kai!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Na aara yarda da wannan azancin zance na IYA RUWA FIDDA KAI a lamuran Nijeriya. Ga ma wasu kalaman da ke cewa duk wanda ya iya allonsa ya wanke kazalika in ka iya ruwa ka iya laka. In mun tuna lokacin da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta bullo da shirin ba da lada ga masu kwarmato an samu waɗanda su ka yi yunƙurin zama 'yan kwarmaton. A iya sani na akwai wadanda su ka samu matala a wajen aikin su don maimakon su samu la'ada sai su ka samu kasadar ɗaure su ko ma zama…
Read More
Hedikwatar Tsaro na shirin fitar da sunayen ‘yan ta’addan da take nema ruwa a jallo

Hedikwatar Tsaro na shirin fitar da sunayen ‘yan ta’addan da take nema ruwa a jallo

Daga BASHIR ISAH Alamu na nuni da cewa nan ba da daɗewa ba, Babban Ofishin Tsaro zai saki sunaye da hotunan kwamandojin 'yan fashin dajin da ake nema ruwa a jallo a sassan Nijeriya. Majiyarmu ta tattaro cewar, rundunar soji ta ɗauki matakin yin haka ne biyo bayan bayyanar wasu sabbin shugabannin 'yan ta'addan sakamakon kakkaɓe na da da aka yi. Idan za a iya tunawa, a watan Nuwamban 2022 Babban Ofishin Tsaro ya sanar kan cewa yana neman wasu kwamandojin 'yan ta'addan aƙalla su 19 ruwa a jallo, tare da sanya tukwicin Naira milyan 5 a kan kowannensu ga…
Read More
Allah Ya yi wa Sheikh Surajo Rabi’ah rasuwa

Allah Ya yi wa Sheikh Surajo Rabi’ah rasuwa

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Surajo Rabi'ah, rasuwa a Gusau, babban Jihar Zamfara. Da ƙarfe 6 na yammacin Lahadi ake sa ran za a yi jana'izar marigayin a Masallacin Rabi'ah, inda jama'a za su haɗu don gabatar da sallar janaza. Kawo yanzu, jama'a da dama kuma daga sassa daban-daban ke ci gaba da miƙa saƙonnin ta'aziyya tare da taya 'yan marigayin alhinin wannan rashi. A halin rayuwarsa, marigayin ya yi fice wajen yin da'awa ƙarƙashin Ƙungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iƙamatus Sunna.
Read More
Maraba da watan Ramadana mai albarka!

Maraba da watan Ramadana mai albarka!

Kamar yadda aka sani ne, Allah ya kawo mu watan Ramadana mai albarka, wanda a cikinsa ake gudanar da ibadu masu ninkin lada, waɗanda idan mutum ya aikata su zai kasance yana da lada mai tarin yawan da ya fi waɗanda ya yi in ba a watan ba ne, kamar dai yadda malamai masana ba su ƙasa a gwiwa ba a duk lokacin da watan shigo. Shi watan Ramadan wata ne wanda Allah ya wajabta a yi azumi a cikinsa, sannan aka wajabta wasu abubuwa da dama, aka kuma haramta wasu abubuwan da ba haramun ba ne a watan da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta keɓe Dala Biliyan 1.3 don aikin dogo daga Kano zuwa Nijar

Gwamnatin Tarayya ta keɓe Dala Biliyan 1.3 don aikin dogo daga Kano zuwa Nijar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Sufuri, Said Alkali, ya sanar da wani gagarumin cigaba a fannin samar da kuɗaɗen aikin titin jirgin ƙasa daga Kano-Katsina-Jibiya-Maradi, inda aka samu dala biliyan 1.3 don gudanar da wannan shiri. A wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin jama’a na ministan, Jamilu Ja’afar ya fitar, an yaba da wannan nasarar a matsayin wani muhimmin mataki na inganta alaƙar zamantakewa da tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar. “Dala biliyan 1.3 da aka samu na aikin layin dogo na Kano-Katsina-Jibiya-Maradi babban nasara ne,” inji Alkali. Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta…
Read More
Wasu ’yan mata sun ƙirƙiro janareta mai amfani da fitsari a Nijeriya

Wasu ’yan mata sun ƙirƙiro janareta mai amfani da fitsari a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu matasa huɗu, Duro-Aina Adebola Akindele Abiola, Faleke Oluwatoyin, da Bello Eniola, daga Legas a Nijeriya sun ƙirƙiro janareta mai amfani da fitsari wanda zai iya samar da wutar lantarki. Duro-Aina Adebola, wata matashiya ‘yar shekara 14, ta ce manufar yin amfani da fitsari wajen samar da wutar lantarki ta faro ne a lokacin da ta karanta wani labari game da wani iyali mai mutane biyar da suka rasa rayukansu sakamakon gubar 'carbon monoxide' da suka shaqi hayaqin da ke fitowa a gidan ta janareta lokacin barci. Ta ce lamarin ya dame ta tana…
Read More
An kashe sojoji 15 a Delta – Hedikwatar Tsaro

An kashe sojoji 15 a Delta – Hedikwatar Tsaro

Daga BASHIR ISAH Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya bayyana cewa, jami'ansu 15 sun rasa rayukansu sakamakon rikicin ƙabilanci a Jihar Delta. A cewar ofishin, jami'an da aka kashe sun haɗa da masu muƙamin Manjo 2, Kyaftin 1, sai kuma ƙananan sojoji 12. Ya ƙara da cewa, marigayan sun cimma ajali ne yayin da suka je kwantar da tarzoma na rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙauyukan Okuama da Okoloba da ke jihar a ranar Alhamis da ta gabata. Sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai na rundudunar, Brig. Gen. Tukur Gusau, wadda aka fitar a…
Read More
Akwai hanyoyin bunƙasa arziki a sauƙaƙe da ba kowa ya sani ba – Ƙiru

Akwai hanyoyin bunƙasa arziki a sauƙaƙe da ba kowa ya sani ba – Ƙiru

Daga AMINA YUSUF ALI (Cigaba daga kashi na farko) Assalamu Alaikum, barkan mu da wannan lokaci. Kamar yadda na yi alƙawari ta hannun Yayata AMINA YUSUF ALI, Wakiliyar Blueprint Manhaja, cewa, idan na samu damar samun wannan shafi na tattalin arziki mai albarka zan bayyana muku wasu hanyoyi da na gano da mutum zai iya zuba kuɗinsa kuma ya samu riba masu kyau in sha Allah. Kamar yadda na fara kwararo wa masu karatu wasu bayanai na daga dabarun da mutum zai yi amfani da su ya samu bunƙasar arziki a rayuwarsa.  A makon da ya gabata mun bayyana cewa, mutum…
Read More