Editor

9513 Posts
Gasar Zakarun Turai: Arsenal da Barcelona sun kai zagayen kusa da ƙarshe

Gasar Zakarun Turai: Arsenal da Barcelona sun kai zagayen kusa da ƙarshe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Arsenal ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da ta yi nasara a kan FC Porto da cin 4-2 a bugun fenariti ranar Talata a Emirates. Tun farko Arsenal ce ta ci 1-0 ta hannun Leandro Trossard saura minti hutu su je hutu, irin wannan sakamakon Porto ta samu a Portugal a wasan farko. Hakan ne ya sa aka yi ƙarin lokaci daga nan aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga. Gunners ta ci ƙwallaye a bugun fenariri ta hannun Odegaard da Kai Havertz da Bukayo Saka da kuma Declan…
Read More
Ƙarancin abinci: CBN ya bada tallafin taki buhu miliyan 2.15 domin raba wa manoma a Nijeriya

Ƙarancin abinci: CBN ya bada tallafin taki buhu miliyan 2.15 domin raba wa manoma a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ma’aikatar noma da wadatuwar abinci ta karɓi buhunan takin zamani guda miliyan 2.15 daga Babban Bankin Nijeriya, CBN. Za a raba takin ne ga manoma domin daƙile hauhawar farashin kayayyakin abinci a ƙasar tare da bunƙasa samar da abinci da kuma wadatarsa. Abubakar Kyari, ministan noma da wadatuwar abinci wanda ya yi jawabi a wajen taro a ranar Laraba a Abuja, ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da CBN bisa wannan karimcin. Kyari ya tabbatar wa Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, cewa za a yi amfani da kayan cikin adalci tare da kai…
Read More
Yadda na wanzar da zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Jigawa – Gwamna Namadi

Yadda na wanzar da zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Jigawa – Gwamna Namadi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yayin da a yankuna da dama na Arewa maso Yamma ake fama da mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma, a Jihar Jigawa kuwa Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya bayyana yadda ya sasanta tsakanin manoma da makiyaya da ke rikici a Ƙaramar Hukumar Guri da ke Jihar Jigawa. Cikin bayanan sa kamar yadda Ofishin Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai na Zamani, wato New Media Office ya bayyana, Gwamna Namadi ya ce, an sanar da shi yadda wani shugaban Fulani ya zama ƙadangaren bakin tulun da ke ke da hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikici…
Read More
Gwaman Kebbi ya yaba wa jami’an kashe gobara

Gwaman Kebbi ya yaba wa jami’an kashe gobara

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya jinjina wa jami'an kashe gobara na tarayya da ke aiki a jihar Kebbi bisa ga gamsuwarsa ga irin ƙoƙarin da su ke yi wajen ceto rayuwa da dukiyoyin al'umma a duk lokacin da wani iftila'in wuta ya tashi a wani waje. Ya bayyana haka ne a garin Birnin Kebbi yayin da yake ƙaddamar da sabuwar motar kashe gobara ta zamani ga jami'an a gidan gwamnatin jihar Kebbi. Ya bayyana cewa yana da kyau su haɗa hannu da takwaransu na jiha don samun nasarori wajen aiwatar da ayyukansu…
Read More
Za mu ci gaba da jajircewa wajen hidimta wa jama’a vangaren kiwon lafiya – Kwamared Yusuf

Za mu ci gaba da jajircewa wajen hidimta wa jama’a vangaren kiwon lafiya – Kwamared Yusuf

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban Asibitin PHC Kabuga, Yusuf Adamu Muhammad Kabuga a Ƙaramar Hukumar Gwale ya bayyan cewa karrama shi da lambar yabo abin farin ciki ne gare shi da ma'aikatan asibitin Kabuga PHC, da sashin lafiya na ƙaramar hukumar Gwale da ma'aikatar lafiya da sauran masu ruwa da tsaki na Kano kamar yadda Kwamared Yusuf Adamu Muhammad ya bayyana a lokacin da ya karɓi kyautar karramawa ga ƙungiyar Health Awareness a makon da ya gabata. Haka kuma Malam Yusuf ya ce aikin lafiya aiki ne na jama'a da ke buƙatar kulawa da nutsuwa, da haƙuri da jajircewa,…
Read More
Zargin cushe a kasafin 2024: Yadda dakatar da Sanata Ningi ta tada ƙura a Nijeriya

Zargin cushe a kasafin 2024: Yadda dakatar da Sanata Ningi ta tada ƙura a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A Nijeriya, jam'iyyun hamayyar ƙasar sun yi Allah-wadarai da matakin da majalisar dattawa ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku, bayan da ya yi wasu kalamai da ke nuna an cusa wasu kuɗi naira kusan tiriliyan huɗu, waɗanda ba a san inda aka nufa da su a kasafin kuɗin ƙasar na bana ba. Jam'iyyun hamayyar suna ganin kamata ya yi a fara da gudanar da bincike kan batun cushen kuɗin, don a tabbatar da gaskiya ko akasin zargin, kafin a ɗauki matakin dakatar da ɗan majalisar. Matakin dakatar da…
Read More
Ramadan: Abincin da ya kamata a ci da waɗanda za a ƙaurace wa

Ramadan: Abincin da ya kamata a ci da waɗanda za a ƙaurace wa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Miliyoyin Musulmai a faɗin duniya sun fara azumin watan Ramadana, ɗaya daga cikin watanni masu tsarki a addinin Musulunci. A lokacin Sahur (kafin alfijir) da kuma buɗa baki (magariba), yana da kyau a san takamaiman nau'ikan abincin da ya kamata a ci don tabbatar da ɗorewar kuzari da jin daɗin rayuwa gabaɗaya. Abubuwan da ya kamata a ci lokacin Sahur: A yayin Ramadan idan kana son ka yini da kwarinka da lafiya shi ne a ci abinci mai gina jiki, da sauransu, kuma dole ka sha ruwa sosai. A kuma ci abinci mara nauyi mai lafiya…
Read More
Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

Ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ya yi Allah-wadai da kisan da Isara’ila ke yi wa Falasɗinawa

*Ya nuna alhini kan sace ɗaliba a arewacin Nijeriya Daga BASHIR ISAH Ofishin Jakadancin Falasɗinu a Nijeriya ƙarƙashin Abdullah M. Abu Shawesh, ya tir da irin kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, ofishin ya fara bayani ne da nuna alhininsa kan ɗaliban da aka sace da sauransu a yankin Arewa. Abdullah M. Abu Shawesh ya ce, "Jin irin wannan labari yana motsa ni sosai kuma yana ƙara baƙin cikina "A cewar dokar Yahudawa, dole ne a kashe dukkan mazauna Gaza." "Hukumomin Isra'ila sun amince da wannan nau'in tunzura jama'a, kuma…
Read More
RTEAN ta ƙaddamar da sabbin shugabannin Legas

RTEAN ta ƙaddamar da sabbin shugabannin Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar ma’aikatan motocin sufuri ta qasa (RTEAN) reshen jihar Legas ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar ta ƙasa. Ku tuna cewa an dakatar da ayyukan RTEAN a jihar Legas sama da watanni 15. Bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi, an shawo kan lamarin wanda ya kai ga sake fasalin shugabannin ƙungiyar a jihar. A lokacin da yake jawabi ga sabbin zaɓaɓɓun shugabannin a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Shugaban RTEAN, Musa Maitakobi ya umarcesu da su daina karya doka da oda da kuma kiyayewa a yayin gudanar da ayyukansu. Ya ƙara…
Read More
Kwastom ta kama bindigogin da aka yi safararsu ta ɓarauniyar hanya a Legas

Kwastom ta kama bindigogin da aka yi safararsu ta ɓarauniyar hanya a Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa (NCS) da ke Tin-Can Island a Legas, ta kama bindigogi da sauran kayayyakin da ake zargin wasu ɓata-gari sun shigo da su ta haramtacciyar hanya. Majiyarmu ta ce sauran kayayyakin sun haɗa da rigunan sojoji haɗi da miyagun ƙwayoyi. An ce Kwastom ta kama kayayyakin ne yayin da take duba kayayyakin da aka shigo da su daga ƙetare a tashar jirgin ruwa na Tin-can. Sai dai babu cikakken bayani a kan ko an samu kama wani ko wasu da ke da alaƙa da kayayyakin. Kama kayan na zuwa ne watanni takwas…
Read More