15
Mar
Firaministan Haiti Ariel Henry ya yada ƙwallon mangoro domin hutawa da ƙuda, wajen miƙa murabus ɗinsa a matsayin shugaban ƙasar da ke yankin Caribbean, bayan cimma matsaya da ƙungiyar ƙasashen yankin a matsayin mafita na warware rikicin siysar ƙasar. Shugaban ƙungiyar ƙasashen yankin Caribbean kuma shugaban ƙasar Guyana Irfaan Ali, wanda ya tabbatar da shirin murabus din Henry, ya yaba da matakin da ya kira wata dama ta kafa kwamitin shugaban ƙasa na riqon ƙwarya wanda zai naɗa firaministan riƙon kwarya. Henry mai shekaru 74 wanda ke riƙe da kujerar firanministan Haiti da ba zaɓen sa aka yi ba tun…
