11
Jun
Shugaban ƙasar Malawi Lazarus Chakwera ya faɗa ranar Talata cewa ba a samu wanda ya rayu ba a cikin jirgin da ke ɗauke da mataimakinsa Saulos Chilima da kuma wasu mutum tara lokacin da jirgin su ya faɗi a wani daji. Masu neman jirgin sun sami nasarar gano ɓarguzan jirgin lokacin da a ka nemi jirgin ba a gani ba. Jirgin an neme shi ba a ganshi ba jiya Litinin lokaci da yakamata ya sauka a wani gari Mzuzu da ke arewacin ƙasar amma ya gaza hakan sabida yanayi marar kyau. Wasu hotuna da gidan Jarida na AfP ya fitar…
