ukarofi

12547 Posts
An dakatar da shugaban APC na Kebbi da na ƙaramar hukumar Zuru

An dakatar da shugaban APC na Kebbi da na ƙaramar hukumar Zuru

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta sanar da dakatar da Alhaji Abubakar Muhammad Kana-Zuru shugaban Jam'iyyar APC na jihar da kuma Honarabul Aliyu Abubakar Abiola shugaban Jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Zuru bisa zarge-zargen karya dokokin jam’iyya da rashin gudanar da ayyukan jam’iyya yadda ya kamata.Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Sakataren jam’iyyar na jihar, Alhaji Sa’idu Muhammad Kimba ranar Larabar nan. Takardar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe daga masu ruwa da tsaki a yankin masarautar Zuru. Ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da rashin himma wajen gudanar…
Read More
JIBWIS ta naɗa Bashir Tanimu a matsayin uban ƙungiya a Katsina

JIBWIS ta naɗa Bashir Tanimu a matsayin uban ƙungiya a Katsina

Kwamitin Ilimi na ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Katsina ta naɗa Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Mallam Bashir Tanimu Gambo, a matsayin Grand Patron na Jihar Katsina. An gudanar da bikin naɗin ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban JIBWIS na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautus Sunnah), tare da halartar malamai da sauran manyan baƙi. A cewar shugabannin ƙungiyar, an yi wa Mallam Bashir Tanimu Gambo wannan naɗi ne bisa la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa addinin Musulunci da tallafa wa harkokin ilimi, da'awa da sauran ayyukan alheri a faɗin jihar. Da…
Read More
Kansilolin APC sun yi barazanar janye goyon bayansu idan ba a daina zargin Sanata Yari ba

Kansilolin APC sun yi barazanar janye goyon bayansu idan ba a daina zargin Sanata Yari ba

Ƙungiyar National Progressives Councillors’ Forum (NPCF), wadda ke wakiltar kansiloli 10,378 na jam’iyyar APC a faɗin Najeriya, ta yi kira ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya umarci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da na tsaro na tarayya su dakatar da duk wani bincike ko mataki da ake ɗauka kan koke-koken da ƙungiyar ta bayyana a matsayin marasa tushe kuma masu ɗauke da manufofin siyasa kan Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, Marafan Sakkwato. A wata sanarwa da aka fitar bayan taron kwata-kwata na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kano, NPCF ta yi Allah-wadai da abin…
Read More
Matsalar warin ƙafa

Matsalar warin ƙafa

Daga AISHA ASAS  Daya daga cikin matsalolin da likitoci suka ce sun fi yawaita a matsalar ƙafa ita ce warin kafa. Masana sun bayyana cewa, warin ƙafa ba wai zufa kadai ke haddasawa ba, illa haɗuwar zufa da ƙwayoyin cuta da ke rayuwa a fata ko cikin takalma. A cewar masana, idan mutum ya saba sanya takalma rufaffe na tsawon lokaci ba tare da barin ƙafa ta sha iska ba, hakan na ƙara haddasa warin kafa. Likitan fata Dakta Hafsat Bello ta ce: “Warin ƙafa na iya shafar kuzarin mutum da mu’amalarsa da jama’a. Amma abu ne da za a…
Read More
Ku kama sana’a, mata

Ku kama sana’a, mata

Daga AISHA ASAS Mai karatu, sannunku da jimirin bibiyar shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. A shekarun baya, an daɗe ana kallon mace a matsayin mai kula da gida kawai, wadda aikinta ya taƙaita ga girki, rainon yara da kula da miji. Sai dai sauyin zamani, hauhawar farashin kayayyaki da matsin tattalin arziki sun sauya wannan fahimta a hankali, har ta kai ga yau dubban mata ke rungumar sana'o'i daban-daban domin tallafa wa kansu, iyalansu da ma al'ummar da suke rayuwa a cikinta. Ba wai neman abin duniya kawai ne ya jawo wannan sauyi ba. A'a, mata da dama sun…
Read More
Muhammadu Abbas (1903-1919): Sarkin da Turawa suka fara naɗawa a Kano

Muhammadu Abbas (1903-1919): Sarkin da Turawa suka fara naɗawa a Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sarki Muhammadu Abbas shi ne sarki na 51 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 9 a jerin sarakunan Fulani, har wayau kuma shi ne sarki na farko da Turawa suka fara naɗawa. Sarki Muhammadu Abbas mutum ne jarumi, kuma mai faɗa ba fasawa ko kuma ana iya cewa mutum ne kaifi ɗaya. Ya kasance sarki mai haƙuri da jama’arsa. Sarki Abbas ya yi mulki tare da Turawa, saboda haka hakimansa suka samu dama ta dalilin haƙurinsa da kawaicinsa suna iya yin magana kai tsaye da Turawa, har sai da ta kai jallin munafurci ya…
Read More
Tsoro mai kyau da tasirinsa ga kyawawan ɗabi’u

Tsoro mai kyau da tasirinsa ga kyawawan ɗabi’u

Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D Gabatarwa: Tsoro yana da nau’o’i biyu a rayuwar ɗan Adam. Akwai tsoro mara kyau wanda ke hana mutum ci gaba, akwai kuma tsoro mai kyau (positive fear) wanda ke taimaka wa mutum ya guji kuskure kuma ya rungumi kyawawan ɗabi’u. A cikin addini da zamantakewa, tsoro mai kyau yana taka muhimmiyar rawa wajen gina hali nagari, hana aikata laifi da kuma tabbatar da zaman lafiya a iyali da al’umma. Ma’anar tsoro mai kyau Tsoro mai kyau shine jin tsoron aikata abin da zai jawo fushin Allah, ko cutar da kai ko al’umma, tare da…
Read More
Tsuntsaye na yi wa manonan rani barazana a Kebbi

Tsuntsaye na yi wa manonan rani barazana a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Manonan rani sun koka bisa yadda waɗansu tsuntsaye ke yi musu barazana ga amfanin gona a Kebbi. Alhaji Musa Najada ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin manoma a jihar Kebbi ya bayyana cewa waɗannan tsuntsayen suna yi musu barazana ga amfanin gona musamman shinkafa a daidai wannan lokacin da suke daf da soma girbi wanda yanzu ya zama dole ga manomi ya yi Sallar asuba gona idan ba haka ba abinda zai samu sai dai rauno (ciyawa) saboda za ka ga ayarin su kamar hadari sun fi dubu kuma duk inda suka sauka kafin minti ɗaya…
Read More
An yi jana’izar waɗanda suka rasu a rikicin Gulma

An yi jana’izar waɗanda suka rasu a rikicin Gulma

Daga JAMIL GULMA a Kebbi An gudanar da jana'izar waɗanda suka rasu sanadiyyar faɗan makiyaya da manoma a garin Gulma a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu.Da ya ke jawabi gabanin jana'izar, mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar a madadin gwamna Nasir Idris, ya bayyana alhinin gwamna bisa ga wannan lamarin.Ya kuma yi addu'ar Allah ya jiƙan wadanda suka rasu tare da fatan Allah ya bai wa iyalan su da masarautar Kabi haƙurin jure wannan rashin .Ya kuma tabbatar musu da cewa za a zaƙulo duk wanda ke da hannu a cikin wannan aika-aikar tare da hukumta su kamar…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira da a cigaba da fatattakar ‘yan bindiga

Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira da a cigaba da fatattakar ‘yan bindiga

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar dokokin jihar Katsina ta yaba da ƙoƙarin Gwamnati na kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da yin kira da a ƙara ƙaimi wajen dawo da zaman lafiya jihar. A zaman wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar dokokin Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, majalisar ta maida hankali kan matsalolin tsaro da suka shafi wasu yankunan jihar. An gabatar da ƙudurin haɗin gwiwa da shugaban masu tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, mai wakiltar mazaɓar Matazu kuma bulaliya na majalisar ya jagoranta, tare da mataimakin shugaban masu tsawatarwa, Hon. Salisu Hamza Rimaye, mai wakiltar mazabar…
Read More