Daga AISHA ASAS
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai 3,810 da suka samu sakamako mai kyau na auna fahimtar SSCE da aka yi musu kuɗin rajistar UTME.
Haka nan, gwamnan ya amince ya biya kuɗin jarrabawar NABTEB ga ɗalibai 1,751 da ke ajin ƙarshe a makarantun fasaha da ke jihar, da kuma ɗalibai 499 daga makarantun koyon Larabci da ke shirin rubuta jarrabawar NBAIS bayan su ma an auna fahimtarsu.
Bugu da ƙari, gwamnan ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai 11,580 da suka samu sakamako mai kyau na gwajin da aka yi musu, kuɗin jarrabawar NECO.
Takardar sanarwar manema labarai da Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr. Aliyu U. Tilde ya fitar, ta nuna baki ɗaya kuɗi milyan N185,580,550.00 gwamnan zai kashe wajen cika wanan ƙudiri.
Kwamishinan ya ce ya zuwa yanzu, hukumomin jarrabawar nan uku ba su bin gwamnatin jihar bashin ko taro. Tare da cewa Gwamnan Bala ya bada odar kammala biyan kuɗaɗen wannan karo ya zuwa ƙarshen Agusta mai zuwa.
Da wannan ne, kwamishinan ya ce akwai buƙatar ɗaliban da lamarin ya shafa su hanzarta su mallaki Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) kafin a kai ga biyan kuɗin a banki. Ya ce shirye-shirye sun kankama game da yadda za a yi wa ɗaliban rajista a ƙananan hukumominsu.
Yana mai cewa gwamnati ta shirya biyan kuɗin duk dalibin da ya mallaki lambar NIN, da zarar ɗalibi ya nuna lambarsa za a miƙa masa fom ɗinsa.