Bikin Sallah: Sufeto Janar ya ba da umarnin a matse ƙaimi game da sha’anin tsaro

Daga AMINA YUSUF ALI

Babbab Sufeton ‘Yan Sanda Mr Usman Baba, ya ba da umarnin a inganta sha’anin tsaro a faɗin ƙasa albarkacin bikin Babbar Sallah na bana.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na ƙasa, Mr Frank Mba, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Lahadi a Abuja.

Baba ya buƙaci kwamishinonin ‘yan sanda a faɗin ƙasa da mataimakansu da su tabbatar an bi umarnin nasa sau da ƙafa.

Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin hana aukuwar kowane irin akasi a sassan ƙasa a lokacin bikin sallah.

Don haka ya bai wa manyan jami’an rundunar na shiyyoyi da ma ƙasa baki ɗaya umarnin ɗaukar ƙwararan matakan tsaron da suka dace domin tabbatar da lumana a faɗin ƙasa yayin bikin Idil Kabir.

Umarnin da Sufeton ya bayar ya haɗa da tura jami’ai da kayayyakin aiki su yi sintiri a muhimman wurare da suka haɗa da manyan hanyoyi, wuraren ibada, wuraren shaƙatawa da dai sauransu.

Sai dai, Baba ya yi gargaɗin cewa dole jami’an da za baza a ƙasa su zamana ƙwararru masana makamar aiki waɗanda za kula da ‘yancin ‘yan ƙasa daidai da ƙa’idojin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *