Buhari zai karrama Tinubu da Shettima da manyan lambobin yabo na ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Alhamis, 25 ga Mayu, 2023, ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai karrama zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, da kuma Kashim Shettima, Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Tinubu dai za a ba shi babban kwamandan oda na Tarayyar Nijeriya (GCFR) yayin da Shettima za a karrama shi da Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).

Tolu Ogunlesi, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin sadarwar zamani da sabbin kafafen yaɗa labarai, ya sanar da ci gaban a ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *