Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Jaruma a Kannywood, Saratu Giɗaɗo ta riga mu gidan gaskiya

Da Ɗumi-ɗumi: Jaruma a Kannywood, Saratu Giɗaɗo ta riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH da RABI'U SANUSI Allah Ya yi wa fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka di sani da Daso, rasuwa. Jarumar ta rasu ne a ranar Talata kamar yadda wani makusancinta ya bayyanawa MANHAJA. Da yake amsa tambayar wakilinmu, makusancin marigayiyar ya ce lafiya ƙalau Saratu ta wayi gari a wannan rana. Ya ƙara da cewa, hasali ma Mmarigayiyar ta ɗauki azumi a wannan rana. Har wa yau, wata majiyar ta sheda ma wakilinmu cewa, "Saratu Gidado tana fama da rashin lafiya a tsaitsaye ne, wanda a yau kuma ta yi mutuwar Fuj'a".…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta ƙara hutun Ƙaramar Sallah

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara hutun Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta amince da ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, 2024, a matsayin ƙarin hutun aiki domin bukukuwn Ƙaramar Sallah. Bayanin haka na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya. Da fari, rakunan Talata da Laraba na wannan makon Gwamnatin ta ayyana a matsayin ranakun hutu don bikin salla, amma daga bisani ta ƙara zuwa Alhamis sakamon Ƙaramar Sallah ta faɗa Laraba. Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar musulmi murnar kammala wata guda na…
Read More
Abin da Shugaban NFC, Ali Nuhu suka tattauna da Jakadan Spaniya a Nijeriya

Abin da Shugaban NFC, Ali Nuhu suka tattauna da Jakadan Spaniya a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin ta wannan makon Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai ta Ƙasa (NFC), Dokta Ali Nuhu, ya yi ganawa ta musamman a Abuja tare da Jakadan Ƙasar Spaniya a Nijeriya, Juan Ignscio Sell, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa. Tattaunawar tasu ta shafi samar da ƙawance tsakanin NFC da Spaniya domin bunƙasa harkokin masana'antar ƙirƙire-ƙirƙire a Nijeriya. Da yake jawabi, Ali Nuhu ya yaba wa Jakada Sell bisa goyon bayan da ofishinsa kan bai wa masana'antar, tare da neman ya faɗaɗa goyon bayan nasa zuwa ga hukumar NFC don bunƙasa harkar shirya fina-finai da sauransu a Nijeriya.…
Read More
Bikin Sallah: KAROTA ta gargaɗi ma su ganganci da abin hawa

Bikin Sallah: KAROTA ta gargaɗi ma su ganganci da abin hawa

Daga RABI'U SANUSI a Kano Hukumar Kula da Zirga-zirgar Abubuwan Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta haramta guje-guje da ababen hawa a lokutan bikin Ƙaramar Sallah a faɗin Jihar. Hukumar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Kakakinta, Nabilusi Abubakar Kofar Na'isa, ya aiko wa MANHAJA a ranar Litinin, inda ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon yadda guje-guje da ababen hawa ke zama barazana ga rayuwar al'umma. "Hakan ne ya sa hukumar ta ce za ta girke jami'anta guda 1500 domin sa ido a shagulgulan bikin Sallah a lungu da saƙo na jihar, domin su…
Read More
An ga watan Ƙaramar Sallah a Nijar

An ga watan Ƙaramar Sallah a Nijar

Daga BASHIR ISAH Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce an ga watan Ƙaramar Sallah a wasu jihohi biyar na ƙasar. Don haka, Talata take 1 ga Shawwal kuma ranar Ƙaramar Sallah a ƙasar. Sai dai, maƙwabciyar Nijar, wato Nijeriya da Saudiyya da sauransu, aun ce ba su ga wata ba, wanda hakan ya sa za su yi azumi 30 a ƙasashen sannan Laraba su yi Ƙaramar Sallah.
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ba a ga watan Ƙaramar Sallah ba a Nijeriya — Sarkin Musulmi

Da Ɗumi-ɗumi: Ba a ga watan Ƙaramar Sallah ba a Nijeriya — Sarkin Musulmi

Daga BASHIR ISAH Sarkin Musulmi, Alh Abubakar Sa'ad, ya tabbatar da cewa ba a jinjirin watan Shawwal ba a Nijeriy a wannan Litinin ɗin. Don haka ya buƙaci al'ummar Musulmi ƙasar su cika azumi watan Ramadan zuwa 30, ta yadda ya zuwa Laraba, 10 ga Afriluu 2024, sai a yi bikin Ƙaramar Sallah. Da wannan, ya tabbata cewa Laraba ce 1 ga watan Shawwal, 1445AH. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Kwamitin bai wa Sarkin Musulmi Shawar kan lamurran addini ya fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Fargesa Sambo Wali Junaidu, wanda shi ne…
Read More
Bikin Sallah: Duk gidan wasan da ya aikata ba daidai ba a Kano zai rasa lasisinsa — El-Mustapha

Bikin Sallah: Duk gidan wasan da ya aikata ba daidai ba a Kano zai rasa lasisinsa — El-Mustapha

Daga RABIU SANUSI A ƙoƙarin sa na tabbatar da ana bin dokoki sau da ƙafa, Shugaban Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta jihar Kano. Abba El-mustapha, ya kafa wani kwamiti na musamman wanda zai lura da yadda gidajen wasanni a Kano zasu gudanar da shagul-gulan bikin ƙaramar sallah. El-mustapha ya wannan jawabin ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da shugabancin kwamitin da mambobinsa, ƙarƙashin jagoranci daraktan kuɗi da mulki na Hukumar, Alh. Abdulkarim Badamasi, sai darakta mai lura da sashin shirya fina-finai, Alh. Idiris Zakari Ya'u Zaura. Sauran sun haɗa da Daraktan kula da sashen ɗab'i, Alh Abubakar Zakari Garin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Laraba Saudiyya za ta yi Ƙaramar Sallah

Da Ɗumi-ɗumi: Laraba Saudiyya za ta yi Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa, ya zuwa ranar Laraba, 10 ga watan Afrilun 2024 za a yi Ƙaramar Sallah a ƙasar. Ta ce hakan ya faru ne sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin wanda hakan ya sa za a yi azumin Ramadan 30 a ƙasar. Kafin wannan lokaci, masana da masu bincike a fagen ilimin taurari sun ce da wahala a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin saboda yanayin tafiyar duniyar wata da ta rana. Da wannan, ya tabbata Laraba ce 1 ga watan Shawwal, 1445AH a ƙasar Saudiyya.
Read More
Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH Tsigaggen Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi watsi da matakin da Majalisar Dokokin Jihar ta ɗauka na tsige shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar. Shaibu ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗan bayan da majalisar jihar ta sige shi. A ranar Litinin Majalisar Dokokin Jihar Edo ta tsige Shaibu daga muƙamin nasa bayan da ta karɓi rahoto kan binciken da aka gudanar a kansa, kana ta maye gurbinsa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo. Majalisar ta kafa…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH An naɗa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo. Naɗin nasa ya biyo bayan tsige Mataimakin Gwamnan mai barin gado, Philip Shaibu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi ne. Omobayo injiniya ne a fannin lantarki kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Akoko-Edo da ke jihar. An tsige Shaibu a muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne yayin zaman da majalisar ta yi a ranar Litinin. Majalisar ta ɗauki matakin tsige Shaibu ne bisa shawarwarin Kwamitin Binciken da ya gudana ƙarƙashin Justice S.A. Omonua-led mai murabus, binciken da aka gudanar bayan da Majalisar jihar…
Read More