23
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Reshen Jihar Zamfara na ƙungiyar malamai matasa don wa'azi da faɗakarwa, (Zamfara United of Youth Scholars for Preaching and Guidance) yau Lahadi sun gudanar da zaman addu'o'i na musamman don samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nasarar Sanata Abdulaziz Abubakar Yari a matsayin darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027. An gudanar da zaman addu'o'in, a zauren taro na Maryam Multi-Purpose Hall da ke Gusau, babban birnin jihar. Taron ya samu halartar malamai da ɗalibai daga faɗin jihar. Da yake jawabi a wurin taron, shugaban ƙungiyar, Malam Naziru Ibrahim…
