23
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sa’o’i kaɗan bayan tabbatar da nasarar samun wa’adin mulki na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Adeleke, wanda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, a zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Yayin da yake gode wa…
