Labarai

Yadda hukumar bogi ta gina tsarin gudanarwa a jihohi 20 da ofisoshi a Amurka da Chana

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'National Brands Development and Made in Special Project Offic', wadda aka zarga da "hukumar bogi", ta kasance ta faɗaɗa tsarin gudanarwarta a jihohin Nijeriya 20 da wasu manyan ƙasashe guda biyu gami da samar da kodineta ja ƙasa, daraktocin shiyyoyi, kodentocin jihohi da wakilai a Amurka da Chana, kamar yadda binciken jaridar NewsPointNigeria ya nuna. A wani bincike da aka gudanar a shafinta na intanet a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, an gano cewa Hon. Nwabueze George shi ne shugabanta kuma kodineta na ƙasa tare da daraktan gudanarwa na ƙasa, daraktocin shiyyoyi uku,…
Read More
Masarautar Koko ta nemi a sauƙaƙa aure

Masarautar Koko ta nemi a sauƙaƙa aure

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Mai girma uban ƙasar Koko, Alhaji Mohammed Bello Koko II, ya bayyana aniyar masarautar Koko na farfaɗo da dokokin da za su taimaka wajen sauƙaƙa yin aure ga matasa da kuma masu son ƙara mata ta hanyar rage nauyin kuɗi da al’adun da ke ƙara tsadar aure. Basaraken ya bayyana cewa tun da farko akwai irin wannan doka a masarautar Koko wacce manufarta ita ce kare matasa daga shiga cikin matsanancin nauyin da zai iya hana su yin aure ko kuma ya sa su fara rayuwar aure cikin matsalolin bashi ko faɗawa tarkon shaiɗan. Insha…
Read More
Jam’iyyar APC a Zamfara ta yaba da naɗin Yari da Matawalle jami’an kamfen ɗin Tinubu

Jam’iyyar APC a Zamfara ta yaba da naɗin Yari da Matawalle jami’an kamfen ɗin Tinubu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen Jihar Zamfara ta bayyana naɗin Sanata Abdulaziz Yari Abubakar da ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle a matsayin shugabannin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban ƙasa na 2027. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar, Ibrahim Muhammad ya sanya wa hannu yau Asabar, shugaban jam'iyyar na jihar Hon. Kabiru Moyi Birnin Magaji, ya bayyana cigaban a matsayin wata alama mai kyau ga jam'iyyar kafin babban zaɓen ƙasa. Hon. Moyi ya ce mambobin jam'iyyar APC a Zamfara suna da cikakken ƙwarin gwiwa cewa shigar shugabannin Zamfara biyu ba…
Read More
Za mu nemi wa’adi na biyu ne bisa nasarorin da muka samu – Gwamna Raɗɗa

Za mu nemi wa’adi na biyu ne bisa nasarorin da muka samu – Gwamna Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta nemi goyon bayan al’umma domin sake komawa wa’adi na biyu ne bisa ayyukan da ta gudanar da nasarorin da ta samu, ba wai ta hanyar yin sabbin alƙawurra ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin ƙaddamar da masu gudanar da ayyukan APC Zalla Movement a ƙananan hukumomi 34 da mazaɓu 361 na jihar Katsina, wanda aka gudanar a People’s Square, Katsina, domin ƙara ƙarfafa tsarin jam’iyyar APC tun daga matakin ƙasa. Gwamna Raɗɗa ya ce nasarorin da gwamnatinsa…
Read More
Gimbiya Elayo ta kira al’umma su kare aikin ACReSAL a Nasarawa

Gimbiya Elayo ta kira al’umma su kare aikin ACReSAL a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gimbiya Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa kuma shugabar kwamitin gudanarwa na aikin ACReSAL a jihar Nasarawa ta yi kira na musamman ga al’ummomin da suka amfana a faɗin jihar da su ɗauki nauyin kiyayewa da kula da kuma kare dukkan ayyukan da aka yi musu ta hanyar ayyukan "Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes" (ACReSAL) a turance wato wani shiri na musamman dake kare muhalli da kuma rayukan al"umma musamman a yankunan karkara domin cigaba mai ɗorewa. Dr. Elayo ta yi wannan kiran ne a ranar ƙarshe na yawon duba ayyukan ACReSAL…
Read More

Babban Limamin masallacin Anas Bin Malik Islamic Centre ta Abuja ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar yau Asabar ne Dakta Ibrahim Mohammed Fadul da aka fi sani da Imam Abuya ya rasu. Marigayin, wanda shi ne babban Limamin Masallacin Cibiyar Anas Bin Malik Islamic da ke yankin rukunin gidajen AMSSCO Platinum City a Galadimawa, ya rasu ne a Abuja bayan fama da wani rashin lafiya. An kuma shirya gudanar da jana'izarsa da misalin ƙarfe 1:30 na rana a Babban Masallacin Ƙasa da ke yankin Central Area a babban birnin. Allah SWT ya jiƙansa ya kuma gafarta masa kurakuransa tare da bai wa makusantansa haƙurin juriya ga rashinsa.
Read More

‘Yan bindiga sun sace masu ibada bayan sallar Juma’a a ƙauyukan Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutane a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Borgo ta Jihar Neja, ciki har da waɗanda suke kan hanyar koma wa gidajensu bayan kammala sallar Juma’a. Al'amarin ya auku ne a ranar Juma’a a jim-kaɗan bayan kammala Sallar Juma’a a babban masallacin ƙauyen Dekara, inda wasu 'yan bindiga suka far wa jama'a tare da yin awon-gaba da masu ibada daga ƙauyukan Gidan Zana, Masaka da Sabon Gida. Daga cikin waɗanda aka sace akwai wani dattijo mai shekara 90 wanda mahaifi ne ga Dagacin Dekara, lamarin da ya jefe…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya naɗa kansa shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓensa a ƙarƙashin Jam'iyyar APC yayin tunkarar babban zaɓen 2027. Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya fitar da jaddawalin mambobin a wata takarda da ya fitar a yau Asabar. Kwamitin ya ƙunshi; Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar, Hope Uzodimma a matsayin sakatare sai Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a muƙaman shugaba da mataimaki. Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman sune mataimakan sakatare na ɗaya da ta biyu. A cewar sanarwar, shugaban kwamitin, Shugaba Tinubu zai yi aiki…
Read More

Sanatan APC da gwamnan Kwara ya kayar a zaɓen fidda gwani ya samu tikiti a PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rikicin siyasa da ya dabaibaye jam'iyyar APC a Jihar Kwara ya ɗauki wani salo mai kama da wasan kwaikwayo yayin da Sanata Saliu Mustapha da ke wakiltar Kwara ta Tsakiya ya samu tikitin shiga takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP domin neman kujerar sanatan yankin a zaɓen 2027. Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan sanatan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar mai mulki a hukumance kan wata taƙaddama da Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq da ake ganin ita ta sabbaba ɗaukar matakin nasa. A ranar Juma'a Mustapha ya karɓi fom ɗin PDP don shiga takarar, wanda…
Read More
NSCDC da ma’aikatar muhalli ta Nasarawa sun haɗa kai don yaƙi da shigar yara haƙar ma’adanai

NSCDC da ma’aikatar muhalli ta Nasarawa sun haɗa kai don yaƙi da shigar yara haƙar ma’adanai

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta jihar Nasarawa ta haɗa kai da hukumar tsaro ta NSCDC domin magance matsalar shigar ƙananan yara cikin harkar haƙar ma’adanai tare da kai farmaki kan masu haƙar ma'adanan ba bisa doka ba. An ƙulla wannan yarjejeniyar ne a ranar juma’a yayin wani ziyara na musamman da kwamandan NSCDC na jihar Nasarawa Brah Samson Umorou ya kai wa ofishin kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa Gimbiya Dr. Margaret Elayo. A lokacin zaman Dr. Elayo ta bayyana abubuwan da ta gani da ido a yayin ziyarar tantance illolin muhalli da…
Read More