22
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da aka fara gasar Premier League ta ƙasar Ingila a yammacin ranar Juma'a, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, ta yi nasarar doke Coventry City da ci 3 da 0 a filin wasa na Emirates. Kai Havertz ne ɗan wasan da ya buɗe asusun zura ƙwallo a gasar ta bana bayan samun wata dama a minti na 15 da take wasan, yayin da Coventry ta gaza jure matsin mai masaukin baƙin. Wannan ƙwallo ta ba Arsenal damar cigaba da jan ragamar wasan cikin salo mai ban ƙaye kan Coventry, wadda sabuwar ƙungiya ce a…
