19
Nov
Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci Bankin Bunƙasa Afirka (AfDB) da ya saka Jihar Zamfara cikin shirinsa na taimaka wa shiyyoyin harkokin noma (SAPZ) kashi na biyu. Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron da gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma suka yi da Shugaban AfDB, Dr. Akinwunmi Adesina a ranar Asabar. SAPZ shiri ne mai manufar daƙile fitar kayan gona zuwa ƙetare, maimakon haka ya zamana ana sarrafa su a cikin gida. Sanarwar da Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, Zamfara ba ta…
