Labarai

2024: Gwamnan Jigawa ya gabatar wa majalisa kasafin N298.14bn

2024: Gwamnan Jigawa ya gabatar wa majalisa kasafin N298.14bn

Daga ABUBAKAR MUHAMMAD TAHEER Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Ɗan Modi, ya gabatar da kasafin shekarar 2024 ga 'yan majalisar dokokin jihar a ranar Talata. Namadi ya bayyana cewa kasafin na 2024, za a kashe Naira biliyan 111.98 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. Haka kuma, ya ce an ware kashi 59% cikin 100% wanda adadin sa ya kai Naira biliyan 175.42 domin gudanar da manyan ayyuka a faɗin jihar. Ya ƙara da cewa an yi nazari da taka-tsan-tsan wajen tsara kasafin duba da yadda Dalar Amurka take tashin gwauron zabbi da kuma farashin ɗanyen mai a kasuwannin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumu: Mun tsare waɗanda suka farmaki Ajaero ku yi haƙuri ku janye yajin aiki, Gwamnati ga NLC

Da Ɗumi-ɗumu: Mun tsare waɗanda suka farmaki Ajaero ku yi haƙuri ku janye yajin aiki, Gwamnati ga NLC

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Taryya ta ce a halin da ake cike ta samu nasarar tsare waɗanda Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ci na-jaki a hannusu, don haka ta ce tana bai wa ƙungiyar haƙuri kan ta dubi Allah ta janye yajin aikin da take yi. Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha'anin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, shi ne ya tabbatar da tsare waɗanda lamarin ya shafa wanda ake zargin 'yan bangan siyasa ne. MANHAJA ta rawaito an farmaki shugaban NLC ɗin ne a Owerri, babban birnin Jihar Imo, a ranar 1 ga Nuwamban 2023, a lokacin…
Read More
CBN ya shure wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira

CBN ya shure wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya tsawaita wa'adin amfani da tsaffin takardun Naira, N200, N500 da kuma N1,000 har illa ma sha'a. Daraktan sashen sadarwar bankin, Isa AbdulMumin, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata mai taken, “CBN zai bada damar ci gaba da amfanin da tsaffin takardun Naira a dokance." Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne daidai da yadda hada-hadar kuɗaɗe ke gudana a ƙasashen duniya. Idan za a iya tunawa, a Oktoban 2022 ne CBN ya ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi na N200, N500 da N1000, sannan ya yanka…
Read More
Bankin Musulunci zai kashe wa Nijeriya biliyoyin Dala

Bankin Musulunci zai kashe wa Nijeriya biliyoyin Dala

Daga BASHIR ISAH Bankin Bunƙasa Musulunci (UDB) ya shirya zai kashe wa Nijeriya biliyoyin Dalar Amurka domin aiwatar da ayyukan cigaban ƙasa. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka ranar Talata. Ya ce tallafin ɓangare ne na ribar tattaunawar zuba jari da Shugaba Tinubu ya yi da Mataimakin IDB, Dr. Mansur Muhtar, yayin da suka haɗu a Makka, Saudiyya. A cewar Ajuri, yayin tattaunawar tasu, Tinubu ya ce, "Nijeriya fitila ce da za ta haskaka wa sauran ƙasashen Afirka hanya, kuma da zarar Afirka ta ɗau haske, duniya za ta yi wa al'umma daɗin zama."…
Read More
Tinubu ya yi alhinin rasuwar Samanja

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Samanja

Shugaban Ƙsa Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan tsohon Soja, ma'aikacin yaɗa labarai, kuma fitaccen jarumi, Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta wuce yana da shekaru 84. Shugaban ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan wasan a matsayin babban rashi na mutumin da ya bayar da gudunmuwa ga ƙasarsa a duk wata dama da ya samu ta hanyoyi daban-daban. "Marigayi Pategi dan kishin ƙasa ne da ya zaɓi ya amsa kiran ƙasarsa a lokacin da ta ke buƙatar hidimar sa, shirinsa na talbijin, mai taken Samanja, ya ɗebi ɗimbin shekaru a…
Read More
Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ta yi jimamin mutuwar abokan aikinta a Gaza

Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ta yi jimamin mutuwar abokan aikinta a Gaza

Ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, a ranar 13 ga watan Nuwamba 2023, sun bi sahun takwarorinsu na dukkan tashoshin da ke aiki a duniya domin yin shiru na minti daya domin tunawa da ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da suka rasa rayukansu a yakin da Isra'ila da Hamas ke ci gaba da yi a Gaza. “Yana da matuƙar baƙin ciki cewa muna tare da dukkan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya a duk fadin duniya a dukkan tashoshin da ke aiki don yin shiru na minti daya a yau Litinin, 13 ga watan Nuwamba, 2023 don girmama abokan aikinmu da aka kashe…
Read More
NLC ta tsunduma yajin aiki kan gana wa shugabanta na ƙasa uƙuba

NLC ta tsunduma yajin aiki kan gana wa shugabanta na ƙasa uƙuba

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) da ta 'yan kasuwa (TUC) sun tsunduma yajin aikin gamagari a ranar Talata. Shiga yajin aikin na da nasaba da uƙubar da aka gana wa shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero kwanan nan a Jihar Imo, wanda a cewar ƙungiyar hukumomin da lamarin ya sha sun gaza yin komai kan batun. Daga cikin buƙatun da NLC ta nema dangane da haka, har da neman a hukunta da kuma sallamar jami'in ɗan sandan da ya jagoranci lakaɗa wa Ajaero duka. Haka nan, ta nemi a hukunta wani hadimin Gwamna Hope Uzodinma na yin…
Read More
Wata ƙungiyar Jam’iyyar ANPP da masu ruwa da tsaki sun buƙaci a mara wa Tinubu baya

Wata ƙungiyar Jam’iyyar ANPP da masu ruwa da tsaki sun buƙaci a mara wa Tinubu baya

Daga BASHIR ISAH Wata ƙungiya ta mabobin Jam'iyyar ANPP tare da tawagar masu ruwa da tsaki sun buƙaci 'yan Nijeriya da su bai wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu da gwamnatinsa cikakken goyon baya don cigaban ƙasa. Ƙungiyar ta buƙaci hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a Abuja mai ɗauke da sa-hannun shugabanta, Malam Kabiru Muhammad Gwangwazo. Da yake tsokaci kan nasarar da Tinubu ya samu a Kotun Ƙoli, Muhammad wanda tsohon shugaban ANPP ne a Jihar Kano, ya yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su rufa wa Tinubu da gwamnatinsa baya don amfanin ƙasa. Ya ce,…
Read More
Zaɓen Bayelsa: Gwamna Diri ya yi ta-zarce

Zaɓen Bayelsa: Gwamna Diri ya yi ta-zarce

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar Jam'iyyar PDP, Gwamna Douye Diri, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Bayelsa. Da wannan, Diri ya samu yin ta-zarce ke nan inda zai cigaba da shugabancin jihar nan da shekaru huɗu masu zuwa. Diri ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 175,196, sannan ɗan takarar Jam'iyyar APC, Sylva, ya rufa masa baya da ƙuri'u 110,108. Sai kuma ɗan takarar Jam'iyyar LP wanda ya zo na uku da ƙuri' 905.
Read More
Sama da mutum 30 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Taraba

Sama da mutum 30 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Taraba

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 32, ciki har da ƙananan yara su 20 da iyaye 12 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya ritsa da su a garin Ibbi, cikin Ƙaramar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba. Bayanai sun ce jirgin da ya yi hatsarin ya yiwo jigilar masunta su sama da 50 daga Ibbi da nufin zuwa gabashin Nijeriya. Hatsarin wanda ya auku a ranar Asabar, ya faru ne a kusa da Zabu da ke iyakar Taraba da Binuwai a Kogin Binuwai. News Point Nigeria ta rawaito wani mazaunin garin Ibbi, Malam Ibrahim Ibbi, ya…
Read More