Babban Labari

Buhari ya bai wa Ministan Ilimi wa’adin makonni 2 ya warware yajin aikin ASUU

Buhari ya bai wa Ministan Ilimi wa’adin makonni 2 ya warware yajin aikin ASUU

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da ya warware yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) suka daɗe suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu. Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karɓi bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin jami’o’i. Idan dai za a iya tunawa, ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta shiga yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran ƙungiyoyin ma…
Read More
Manyan gidajen mai sun yi watsi da farashin gwamnati na Naira 165

Manyan gidajen mai sun yi watsi da farashin gwamnati na Naira 165

*Litar fetur ta koma Naira 185 a Abuja da Kano Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu ababen hawa a Abuja ranar Laraba sun bayyana cewa, an daina samun dogayen layika a gidajen daga jiya Alhamis, inda aka samu ƙarin Naira 20 kan tsohon farashi na Naira 165 a wasu manyan gidajen mai, inda aka wayi gari ya koma Naira 185 maimakon yadda aka saba saye a farashin gwamnati a Kano da Abuja. Kamar yadda rahotanni suka nuna, ranar Laraba a Abuja cewa, ga gidajen mai da yawa da suke a kulle babu mai; sai kuma gidajen da akwai mai…
Read More
Kiran Adamu ga Kiristoci: Ku daina fargaba kan tikitin Musulmi da Musulmi

Kiran Adamu ga Kiristoci: Ku daina fargaba kan tikitin Musulmi da Musulmi

*Sabuwar Gwamnatin APC za ta yi muku adalci, inji Shugaban Jam’iyyar Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci mabiya addinin Kirista da su daina wata fargaba a kan tsayar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2023 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ta APC, wanda ya kasance Musulmi da Musulmi a matsayin shugaba da mataimaki da jam'iyyar ta tsayar ƙarƙarshin takarar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya na mai ba su tabbacin samun cikakken adalci, idan har APC ta sake kafa gwamnati a 2023. Shugaban ya ce, yanayin halin da siyasar ƙasar ke ciki…
Read More
Yadda haɗin bakin gidan kurkuku ya sa harin Kuje yin nasara

Yadda haɗin bakin gidan kurkuku ya sa harin Kuje yin nasara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alamu sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata yadda aka haɗa baki da wasu jami'an tsaro musamman na Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali ta Nijeriya (NCS) wajen samun bayanan sirri a harin yammacin ranar Talata a gidan yarin Kuje, inda mutane biyar da suka haɗa da fursunoni huɗu da jami’an tsaron NSCDC suka mutu. An kuma tabbatar da cewa jami’an NCS uku sun samu munanan raunuka.An ce, ’yan ta'addar masu qarfin gwiwa sun yi nasarar gudanar da ayyukansu na tsawon sa'o'i uku tare da samun fursunoni 879 da suka tsere daga ginin. Cibiyar ta…
Read More
Matsin tattalin arziki ya hana mutane da dama sayen ragunan layya bana a Zariya

Matsin tattalin arziki ya hana mutane da dama sayen ragunan layya bana a Zariya

Daga MOHD BELLO HABIB a Zariya Sakamakon matsin tattalin arziki ya hana wasu jama'a da dama sayen ragunan layya bana saboda tsadar da dabbobin suka yi. Da yake zantawa da wakilin Manhaja a Zariya jiya akan farashin dabbobin a bana, dillalin dabbobi da ke Zariya, Alhaji Abdulmumini Alhassan Sarkin Turken Zazzau ya koka akan tsadar da dabbobin suka yi a bana, ya ce kasuwar ba ta tafiya kamar yadda aka saba. Ya ce, qaracin kuɗi a hannu jama'a ya sanya cinikin dabbobin ya tsaya cak, ya ƙara da cewa ga dabbobin jibge amma babu masu saye saboda tsadarsu. Sarkin Turken…
Read More
2022: Bana awo ya kori ragon layya

2022: Bana awo ya kori ragon layya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Layya dai wata ibada ce da ta samo asali tun lokacin Annabi Ibrahim (AS), lokacin da Allah (SWT) ya umarce shi da ya yanka abin yankawa ranar 10 ga Zul-Hajji, wanda shi ne watan 12 kuma watan ƙarshe a shekarar Musulunci. Layya ita ce dabbar da ake yankawa, domin neman yardar Allah daga cikin nau'o'in tumaki da awaki da shanu ko kuma raƙuma, waɗanda suka cika shekarun yin layya, kuma sun kuvuta daga kowane aibi. An sharɗanta yanka dabbar layya a ranar 10 ga Zul-Hajji da yini biyu bayan dawowa daga sallar idi bayan kuma liman…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya rantsar da sabbin ministoci

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya rantsar da sabbin ministoci

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa majalisarsa garambawul a ranar Laraba yayin da ya rage wata bakwai kafin zaɓen 2023. Kazalika, Shugaban ya rantsar da sabbin ministoci guda bakwai waɗanda Majalisar Dattawa ta amince da naɗinsu kwanan nan. Bayan rantsar da su, Buhari ya yi kira ga sabbin ministocin da su ɗauki wannan muƙami da suka samu a matsayin wata dama ta yi wa ƙasa aiki bilhaƙƙi. Sabbin ministocin da aka rantsar ɗin sun haɗa da; Henry Ikoh (Abia), Umana Okon Umana (Akwa-Ibom), Udi Odum (Ribas), Ademola Adegoroye (Ondo), Umar Ibrahim El-Yakub (Kano), Goodluck Nana Opiah…
Read More
Jami’ar NOUN ta yi sabbin naɗe-naɗe

Jami’ar NOUN ta yi sabbin naɗe-naɗe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Gudanarwar Jami’ar NOUN ta Nijeriya, ta amince da naɗin sabon magatakarda, shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe da kuma shugaban ɗakin karatu, na wa’adi guda na shekaru biyar. Sabbin waɗanda aka naɗa sune, Oladipo Adetayo Ajayi a matsayin magatakarda, Malam Nasir Gusau Marafa a matsayin shugaban kula da shige da ficen kuɗaɗe da Dakta Angela Ebele Okpala a matsayin shugaban ɗakin karatu na jami’ar. An miƙa naɗin ga waɗanda aka naɗa a wasiƙu daban-daban na ranar 27 ga watan Yuni, 2022, kuma magatakarda mai barin gado, Felix I. Edoka ya sanya wa hannu. Edoka…
Read More
2023: APC ta ƙaddamar da dakarun matasa a jam’iyyar don tallafa wa Tinubu

2023: APC ta ƙaddamar da dakarun matasa a jam’iyyar don tallafa wa Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dayo Isreal, a Abuja ranar Laraba, ya ƙaddamar da mambobin tawagar dakarun matasan APC. Tawagar za ta jagoranci gyara da rajistar duk ƙungiyoyin goyon bayan APC da matasa suka kafa, gabanin zaɓen 2023. Isra'ila, a lokacin ƙaddamarwar, ya ce, tagawar za ta yi amfani da na'ura mai amfani da fasaha don jawo goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki a babban zaɓen shekara mai zuwa. Ya ƙara da cewa, “za a buɗe sabunta ƙungiyoyin tallafa wa matasa da ɗalibai na tsawon wata ɗaya, daga ranar Juma’a…
Read More
Kiciniyar tikitin mataimakin Tinubu a Arewa maso Yamma

Kiciniyar tikitin mataimakin Tinubu a Arewa maso Yamma

*Gwamnonin yankin sun shiga ganawa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jagororin Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya na shiyyar Arewa maso Yamma sun naɗa tawagar wakilai da za su je su gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, game da zaƙulo wanda zai zame masa mataimaki a babban zaɓen 2023 mai ƙaratowa.  An cimma wannan matsayar ne a wurin taron jagororin shiyyar Arewa ta Yamma, da suka haɗa da gwamnoni, 'yan takarar gwamna, ministoci da sauransu, wanda ya gudana jiya a Abuja. A wata sanarwa da mataimakin shugaban APC na Arewa ta Yamma, Salihu Lukman,…
Read More