29
Jan
Mata a Nijeriya sun koka da yadda ake mantawa da su bayan ’yan siyasa sun samu gwamnati duk da fitowar da suke ƙwansu da ƙwarƙwata wajen kaɗa ƙuri’a a yayin zaɓe. Wannan koke na matan na zuwa ne a daidai lokacin da ake daf da gudanar da zavukan ƙasar na 2023. Wannan matsala ta rashin damawa da mata a siyasa abu ne da ya daɗe yana ciwa wasu mata tuwo a ƙwarya ganin yadda suka ce ana watsi da su a lokacin da siyasa ta yi daɗi. Matan na cewa wataƙila hakan baya rasa nasaba da rashin ba su cikakkiyar…