Ra’ayi

Taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa: Ina mafita?

Taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa: Ina mafita?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu kawo muku wasu ƙarin dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai a ƙasar Hausa, ta yadda surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana. A wancan rubutun da na yi a baya, mun kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci…
Read More
Makomar tallafin fetur a Nijeriya bayan Yunin 2023

Makomar tallafin fetur a Nijeriya bayan Yunin 2023

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa zuwa Yunin 2023, za ta daina biyan kuɗin tallafin fetur da ta saba biya. Ministar kuɗi da kasafi ta ƙasar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin da ta ke gabatar da kasafin na 2023 ga jama'ar ƙasar. Ta bayyana cewa a 2023, gwamnatin ta ware naira tiriliyan 3.36 ne kawai domin biyan tallafin fetur na wata shidan farko na shekarar. Ta kuma ce wannan matakin na tafiya ne da ƙarin wa'adi na watanni 18 na cire tallafin da aka sanar a 2022. A lokacin da take bayani kan gundarin kasafin, ministar ta bayyana…
Read More
An shiga watan taƙaitawa da daina aiki da tsoffin kuɗi

An shiga watan taƙaitawa da daina aiki da tsoffin kuɗi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA An shiga watan taƙaitawa da kuma daina aiki da tsoffin kuɗi. Wannan ya ƙara bayyana ne bayan isa 9 ga watan nan na Janairu inda ya ke ƙa’idar taƙaita fitar da kuɗi a na’urorin kuɗi na ATM a Nijeriya. Babban bankin Nijeriya CBN ya fara aiwatar da sabuwar ƙa’idar da kuma nuna hakan ba zai kawo wata matsala ba a Nijeriya. Tuni hakan na nuna an fara aiki da tsarin nan na rage amfani da takardun kuɗi don haka ya zama ko dai kowa ya yi ƙoƙarin komawa aiki da na’urori ko kuma ya riƙa shan…
Read More
Kawo ƙarshen cutar Kwalara

Kawo ƙarshen cutar Kwalara

A cikin rahotonta na baya-bayan nan, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya ta sanar da jimillar mutane 19,228 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara, ciki har da mutuwar mutane 466 a shekarar 2022. A ra'ayin wannan jarida, wannan lamari ne mai firgitarwa da ya kamata gwamnati ta ɗauki nauyinsa daqile shi a kowane mataki. Kwalara cuta ce da ake saurin kamuwa da ita da ta ke haifar da gudawa da amai. Ana kamuwa da ita daga najasa ta hanyar gurvataccen abinci, abin sha, da rashin tsafta, kuma yana haifar da rashin ruwa a jikin ɗan adam. Yawan masu…
Read More
Yadda karatun jami’a ke neman zama ƙwalele ga talakan Nijeriya

Yadda karatun jami’a ke neman zama ƙwalele ga talakan Nijeriya

Daga HARUNA UMAR JOS Ga dukkan alamu, shekarar 2022 ita ce shekarar ƙarshe da yaron talaka a Nijeriya zai tafi ƙaro karatu a jami'a (University), ganin yadda wasu takardu masu alaqa da wasu daga cikin jami'oin ke nuna yadda ake shirin ninka kuɗin makaranta, ko ma dai na ce an ninka! Ta iya yiwuwa wannan lamari yana da alaƙa da artabun da ke tsakanin gwamnati da malaman jami'o'i. Ko ma dai menene, da gwamnati da ku malamai, ku tuna fa wannan dambarwa taku a kan 'ya'yan talakawa take ƙarewa. Tana ƙarewa ne a kan mutanen da suke neman na sa…
Read More
Taimakon jin ƙai a lokacin sanyi

Taimakon jin ƙai a lokacin sanyi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A lokacin ƙarshen shekara tsakanin watannin Nuwamba da Disamba har zuwa Maris, a kan samu canjin yanayi da ke juyawa zuwa sanyi ke kasancewa da tsanani a wani wajen lokaci zuwa lokaci. A bana dai Hukumar Kula da Yanayin Muhalli ta Ƙasa, Nimet ta bayyana cewa, za a samu yanayin sanyi da hazo mai tsanani a wasu jihohin Arewa wanda ya taso daga yankin hamadar ƙasashen Chadi da Nijar. A cewar rahoton hazon da ke haɗe da ƙura zai shafi jihohin Borno, Yobe, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, da Jigawa za su samu hazo sosai, yayin da…
Read More
Tarbiyyar ’ya’ya mata haƙƙin Allah ne akan iyaye

Tarbiyyar ’ya’ya mata haƙƙin Allah ne akan iyaye

Wannan wani babban al’amari ne da ya tunkaro gidajenmu, wanda ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen tarbitya da addu’a ga ’ya’yansu, musamman ’ya’ya mata. Ita ƙaruwar gida ba a gidan karuwai ta ke ba, ba kuma zaman kanta take yi ba, a’a hasalima yawancinsu a gaban iyayensu suke, kodai suna jami’a, suna kwana a can ko kuma suna gidan iyayensu. A baya idan ka ji an ce wance karuwa ce, to za ka same ta a bariki tana sharholiyar ta, ko dai tana shan taba ko wiwi, amman na yanzu cikin zubin ƙarshen zamani, 'yan mata ne na gida…
Read More
2023: Mun shiga shekarar zaɓe

2023: Mun shiga shekarar zaɓe

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A kwana a tashi ba wuya ko kuma a wani kaulin bai bar komai ba. Ma'ana duk abun da a ka sakawa lokaci to in Allah ya yarda zai zo. A Nijeriya a kan gudanar da babban zaɓe ne bayan shekaru huɗu kuma duk wanda ya samu damar ɗarewa kujerar zartarwa ta gwamna ko shugaban ƙasa to zai zauna na tsawon shekaru huɗu a kan karaga sannan ya sake samun damar sake tsayawa in har ya sake lashe zaɓe ya sake yin shekaru huɗu kan kujera daga nan kuma shikenan wannan damar ta kare. Duk da…
Read More
Nijeriya da ƙasashe 12 mafi ci gaba a Afirka

Nijeriya da ƙasashe 12 mafi ci gaba a Afirka

Wani rahoto na baya-bayan nan da Insider Monkey ya fitar ya nuna cewa Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashe 12 da suka fi samun ci gaba a nahiyar Afirka. A cewar rahoton mai taken, “ƙasashe 12 Mafi Cigaba a Afirka”, Afirka na ɗaya daga cikin nahiyoyin da suka fi arziki a duniya wajen samar da albarkatun qasa. Abin ban mamaki kuma, nahiyar na ɗaya daga cikin yankuna mafi ƙarancin ci gaba a duniya. Ƙasashen da suka shiga jerin sun yi amfani da albarkatun qasarsu wajen inganta tattalin arzikinsu. Irin waɗannan qasashe su ne; Ghana, Zimbabwe, Masar, Maroko, Afirka ta Kudu,…
Read More
Buƙatar duba tsarin shari’ar Nijeriya

Buƙatar duba tsarin shari’ar Nijeriya

Assalam alaikum. Yayin da a Nijeriya ake fuskantar ƙalubale da suka shafi laifukan fyaɗe da cin zarafin mata da ƙananan yara da sauran kasha-kashe marasa dalili, masana harkokin shari’a a matakai daban-daban na ganin yadda tsarin shari’ar ƙasar ya ci karo da al’adu, yanayin zamantakewa da kuma addini. Wannan al’amarin dai ya sake kunno kai ne a daidai lokacin da ake ganin cewa masu aikata muggan laifuffuka kamar fyaɗe, cin zarrafin mata da ƙananan yara, kashe-kashen mutane na ci gaba da cin karen su ba babbaka sakamakon yadda ake ɗaukar tsawon lokaci wajen zartar da hukunci, lamarin da ke sanyaya…
Read More