Ra’ayi

Darajar kuɗin Nijeriya daga 2004 Zuwa 2022

Darajar kuɗin Nijeriya daga 2004 Zuwa 2022

Daga AMINU ƊAN ALMAJIRI Wanda duk ya kalli irin tuƙin da ake yi wa Nijeriya a yau, ya san ana yi mata tuƙin da zai kai ta ga halaka. Da yawa mutane ban sani ba, son zuciya ne ya sa idan Khalifa Muhammad sanusi II ya yi magana a kan shaanyin tattalin arziki da sha'anin mulkin ƙasar nan suke masa ca! Ko kuwa rashin sani? idan rashin sani ne, sai na ce dama masu hikima sun ce, 'Ɗan Adam maqiyin abinda ya jahilita ne'. idan kuwa son zuciya ne, ya kamata kam yanzu su fito su faɗa wa jama'a cewa,…
Read More
Kwankwasiyya JAMB, NECO da WAEC Kyauta: Anya?!

Kwankwasiyya JAMB, NECO da WAEC Kyauta: Anya?!

Daga FATUHU MUSTAFA Wato ina ga Kwankwaso yana abin nan ne da Bature ke cewa 'Clever by half'. Ga wanda bai san me ake nufi da wannan azancin na Bature ba, sai ya nemi Magana Jari ta ɗaya ya karanta labarin 'Mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi Jiɓi (Gumi)'. Ya yi hakan ne ta hanyar gaya wa mutane abinda suke so su ji ko da kuwa ba zai yiwu ba. Musamman tunda ya lura mutane, son ransu ne a gabansu ba son gaskiya ba. Amma in dai mutane gaskiya suke so, da sai su tambaye shi, mun ji za…
Read More
Sasanta tsakanin Hausawa da Fulani zai kawo tsaro a Arewa

Sasanta tsakanin Hausawa da Fulani zai kawo tsaro a Arewa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ashe matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa, na da nasaba da kisan ƙare dangi da Fulani ke yi wa ƙabilar Hausawa? Tun da ake samun ƙalubalen tsaro a jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma, ban taɓa kawo wannan tambayar a raina ba, don ina ganin ba batun kisan ƙare dangi ba ne, tsohuwar rigima ce da aka saba fuskanta tsakanin manoma da makiyaya, ƙalubalen ɗumamar yanayi da ya kai ga cinye burtalolin shanu zuwa filayen gonaki, da kuma uwa uba shigar vata gari cikin harkar satar shanu da…
Read More
Badaƙalar kuɗin harajin bankuna

Badaƙalar kuɗin harajin bankuna

A Nijeriya, batun harajin da bankuna ke cire wa waɗanda suka yi amfani da asusun ajiya wajen tura kuɗi ko cirewa na cigaba da janyo cece-kuce. A makon da ya wuce ne kwamati na musamman da Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa domin gudunar da bincike kan cajin cirewa da ajiyar kuɗi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna ƙoƙarin hana shi yin aikinsa, da kuma hana shi ya mika wa Buhari rahotonsa. Sai dai sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai magana da ywun shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu ya ce…
Read More
Gudaji da fadar Aso Rock: A gano mana gaskiya!

Gudaji da fadar Aso Rock: A gano mana gaskiya!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun 2003 da Shugaba Buhari ya fara neman takarar shugabancin Nijeriya ya ambata batun yaƙi da cin hanci da rashawa ya zama cikin kan gaba a abubuwan da zai yaka matuƙar Allah ya ba shi nasarar lashe zaɓe. Hatta a jawabin kifar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Shagari a jamhuriyya ta biyu, shugaba Buhari ya kawo dalilan amshe madafun ikon da yadda ’yan siyasa suka afka cin hanci da rashawa. A wannan lokacin ta kai ga shugaban amincewa da ɗaure mutane fiye da shekaru 100 a gidan yari don samun su da laifin zarmiya.…
Read More
Batun raba katin zaɓe

Batun raba katin zaɓe

Assalam alaikum. Fara ba da katunan zaɓe na dindindin ga wasu daga cikin masu zaɓe a Nijeriya ya ja hankalin 'yan ƙasa inda kowa ke bayyana ko tofa albarkacin bakinsa. A wannan Litinin din Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Inec ta soma wannan aiki kuma mutanen da za a bai wa katunan su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli. Sai dai kuma duk da irin tsare-tsare da INEC ta ce ta yi, ana ta samun masu ƙorafi da kokawa kan dogayen layuka wajen samun katin, da…
Read More
Barazanar jefa ƙuri’ar ƙananan yara

Barazanar jefa ƙuri’ar ƙananan yara

Ƙuri’ar ’yan ƙasa da shekaru 18 wata ɓarna ce a tsarin zaɓen Nijeriya. Shekarun da suka cancanci shiga zaɓe a ƙasar sune ’yan shekaru 18 zuwa sama. Sai dai a lokacin zaɓe, ana barin yara su kaɗa ƙuri’a a wasu sassan ƙasar. Wani lokaci ma matattu ma suna yin zaɓe. Kuma wannan shine tushen fara rigingimu. Lokacin da aka ba wa yaran da ba su kai shekarun jefa quri'a damar jefa ƙuri'a ba, hakan yana kawo cikas ga sahihancin tsarin zaɓe kuma yana sanya alamar tambaya kan sakamakon aikin. A kwanakin baya, gamayyar ƙungiyoyin farar hula 10 (CSO) sun koka…
Read More
Me ya sa aka dakatar da koyar da ilimin jima’i a makarantu?

Me ya sa aka dakatar da koyar da ilimin jima’i a makarantu?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ba da jimawa ba ne ofishin Ministan Ma'aikatar Ilimi Malam Adamu Adamu ya fitar da wata sanarwa game umarnin dakatar da cigaba da koyar da ilimin jima'i a ƙananan makarantu da sanarwar fara amfani da harshen uwa na gado wajen koyar da yaran makarantun firamare, a tsarin koyarwa na makarantun ƙasar nan. Batutuwan da yanzu haka ke cigaba da ɗaukar hankalin masana ilimi da sauran jama'ar ƙasa. A wannan mako nima ina son yin tsokaci ne game da batun dakatar da koyar da ilimin jima'i a makarantu, kamar yadda taken rubutun ya nuna, domin qara fayyace…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alƙali Baba

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alƙali Baba

Daga NAFI'U SALISU Kamar yadda yake a dokar ƙasa, dukkan wani jami’in tsaro aikinsa shi ne kare rayuka da dukiyar al’ummar ƙasa. Don haka ne ma kowanne ma’aikacin Ɗansanda sai ya yi rantsuwa da littafin addininsa a yayin kama aikinsa na bada tsaro, cewar ya rantse da kundin tsarin mulkin ƙasarsa zai yi aiki a bisa doka da oda, wajen ƙare rayuka da dukiyar al’umma. Babu wata al’umma da za ta rayu cikin aminci face sai da hukuma a cikinta, kasancewar hukuma a cikin al’umma kuma shi ne ginshiƙin tafiyar da rayuwa cikin tsari, ta hanyar bin doka da oda.…
Read More
Me ke kawo taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa?

Me ke kawo taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa?

Daga AMINA YUSUF ALI Masu karatu sannu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da bayanai a kan yadda alaqar tsakanin surukai take ƙara lalacewa a ƙasar Hausa har take zama ma kamar kishi ne tsakaninsu ba wai surukuta ba. Wannan abu ne mai matuar ban mamaki musamman idan muka yi la'akari da yadda alaƙar surukai take jiya a ƙasar Hausa. A zamanin da, ba komai sai kunya da tsakanin surukai a ƙasar Hausa. Kuma mafi yawan lokuta ma a gida guda suke zaune. Amma hakan bai sa ko da wasa suruka ta…
Read More